Shirin "Lafiya jari ce" na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda matsalar shaye-shaye sannu a hankali ke ci gaba da jefa tarin matasa a lalurar hauka ko kuma tabin hankali, matsalar da ke ci gaba da tsananta a sassan Jamhuriyya Nijar musamman tsakanin matasa ko kuma daliban jami’o’i.
Alkaluman ma’aikatar lafiyar Nijar na nuna yadda ake da tarin matasa da yanzu haka ke karbar maganin cutar kwakwalwa galibinsu sakamakon ta’ammali da miyagun kwayoyi ko kuma shaye-shayen zamani.