Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon zai duba batun barkewar cutar zazzabin typhoid a jihar Nasarawa ta arewacin Najeriya, cutar da ke cikin jerin manyan cutukan da ke janyo asarar rayuka da dama a sassan kasar. Shirin ya tattauna da kwararru a fannin kiwon lafiya, wadanda suka yi karin haske a game da cutar da kuma yadda za a kare kai daga kamuwa da wannan shu'umi zazzabi.