Shirin 'Tarihin Afirka' na wannan lokaci ya cigaba da kawo wa masu sauraro tarihin tsohon shugaban kasar Burkina Faso Thomas Sankara, wanda aka yi wa kisan gilla a bakin aiki. Marigayi Thomas Sankara na daga cikin jerin tsofaffin shugabannin nahiyar Afirka da aka yi amannar cewa yana cike da kishin kasa, zalika yana kan turbar samar da gyara a tsarin shugabancin al'umma.