Shirin 'Kasuwa akai miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya duba taron kasa da kasa kan Sauyin Yanayi a birnin Glasgow na kasar Scotland, da anniyar kasashen duniya na rage amfani da duk wani makamashi dangin Manpetur da masana ke cewa na taimakawa wajen dumamar yanayi da gurbata muhalli, inda shirin yayi nazarin kan tasirin wannan lamari ga tattalin arziki.