A makon da ya gabata ne shugaban hukumar kulada kwallon kafa ta duniya FIFA Gianni Infantino, ya bayyana shirin da hukumar ke yi don gudanar da bikin cika shekaru dari da fara gudanar da gasar lashe kofin duniya ta maza, daga cikin tsarin na hukumar FIFA ke yi, ta sanar da yadda za ta gudanar da gasar ta shekarar 2030.