Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya yi nazari ne kan komawar Ahmed Musa Kano Pillars domin ci gaba da taka leda bayan ya raba gari da Al-Nesry ta Saudiya a cikin watan Oktoban bara. Yau Litinin ne sabon dan wasan ke fara atisaye da Kano Pillars a barikin Bukabu da ke birnin Kano, yayin da masharhanta ke cewa, ya daga darajar kungiyar ta "Masu Gida". Dan wasan ya shaida wa RFI Hausa cewa, akwai yiwuwar nan kusa ya koma Ingila da taka leda. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin.