Shirin Duniyar Wasanni tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya yi nazari ne game da karawar da Najeriya za ta yi da Benin a wasan neman tikitin shiga Gasar Cin Kofin Afrika a Kamaru. Super Eagles ta ce, ba za ta yi sakacin da ta yi a wasanta da Saliyo ba. Kazalika Kaften din tawagar ta Najeriya Ahmed Musa ya mayar da martani kan masu cece-kuce game da matakin da kocin tawagar Gernot Rohr ya dauka na gayyato shi don buga wasan. Kuna iya latsa alamar sauti don jin cikakken shirin.