Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan makon tare da Nura Ado Suleiman ya duba tarihi ne, watau shekarar 1996 lokacin da Nigeria ta lashe lambar zinarin ta na farko a gasar wasanin motsa-jiki na Olympics a birnin Atalanta na kasar Amurka. Inda bayan kwashe sama da shekaru 25 gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta cika alkawarin ta na lada da bada tukuicin gidaje ga rukunin ‘yan wasan da suka fidda Nigeria kunya a wancan lokacin.