Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya leka Jamhuriyar Nijar ne domin yin nazari game da wani tsari na korar daliban da suka fadi jarawaba sau biyu. Amma a yanzu an samu wata badakala ta cuwa-cuwar kera takardu na jabu domin sake mayar ire-iren wadannan daliban wata makaranta ta daban.