Shirin Duniyar wasanni tare da Khamis Saleh ya yi duba kan yadda bikin bayar da kyautukan gwarzon dan kwallo ta Ballon d'Or ya gudana a birnin Paris, kyautar da a wannan shekara dan wasan gaba na Faransa da ke taka leda da Real Madrid Karim Benzema ya lashe saboda rawar da ya taka wajen taimakawa kungiyarsa kai labari a mabanbantan gasa cikin kakar da ta gabata. Ayi saurare Lafiya.