Shirin 'Lafiya Jari ce' a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu, ya tabo babban kalubalen da bangaren lafiya ke fuskan ne a kasashen Afrika, na yadda tarin kwararrun likitoci ke ci gaba da yin kaura daga kasashen zuwa Turai ko Amurka da nufin samun ingantacciyar rayuwa, batun da ke ci gaba da kassara bangarorin lafiyar nahiyar. Najeriya ke matsayin kan gaba a yawan likitocin da ke barin kasar a kowacce rana zuwa ketare.