Kamar yadda aka sani, an fara gasar kofin duniya ta 2022 lami lafiya, sai dai al'ummar yankin nahiyar Afrika na kokawa kan yadda wasan ke tafiya, musamman yadda kasashen da ke wakiltar nahiyar suka gaza yin katabus a wasannin farko da suka buga. Sun koka da irin alkalancin wasa musamman a karawar Portugal da Ghana, da kuma yadda masu horarwa suka yi taa kurakurai.