Shirin 'Duniyar Wasanni' a wannan makon ya yi nazari ne akan yadda gasar lik din kasar Saudiya da ake kira da ‘Saudi Pro League’ ke kokarin dauko manyan ‘yan wasan kwallon kafa daga Turai musamman ma daga gasar Firimiyar Ingila. A farkon wannan wannan shekarar ce dai kungiyoyin da ke wannan gasa suka tashi tsaye wajen ganin sun kawo manyan ‘yan wasan kwallon kafa, duk tsadar su kuwa don su farfado da gasar da kuma samar mata da kima a idon duniya.