Shirin "Kasuwa A kai Miki Dole" na wannan makon ya maida hankali ne kan yadda matsalar karancin takardun kudin naira ya shafi al'ummar kasuwanci dama na yau da kullum a Najriya.
Wannan al'amari dai ya haifar da cece-kuce a tsakanin al'ummar kasar, inda wasu ke ganin sauya fasalin kudin a wannan lokaci shine abu mafi dacewa, yayinda wasu keda ban-bancin fahimta akan lamarin.
Kawo yanzu dai matsalar ta fara sauki tun bayan barazanar da kungiyar kwadago ta kasar ta yi na tsunduma yajin aiki.