A yau shirin "Ilimi Hasken Rayuwa" zai duba matsalar rashin iya lissafi ko Mathematic da yawancin Dalibai ke fama da ita a jihar Maradi ta Jamhuriyar Nijar, wacce ke zama babban kalubale ga samun nasarar karatu.
A shekarar da ta gabata kashi 90 cikin 100 na daliban da suka rubuta jarabawar neman shiga Jami’a da makarantun gaba da sakandare su ka fadi bangaren lissafi, wannan ne dalilin da yasa masu ruwa da tsaki tashi tsaye wajen nemo bakin zaren warware matsalar.