A Najeriya ana ci gaba da samun matsalar cutar sankarar mama, cutar d har yanzu babu takamammen maganinta duk kuwa da cewa daya bisa uku na matan duniya na cikin hadarin kamuwa da ita. Har yanzu dai kwararru sun gaza gano aininhin abin da ke haddasa wannan cuta, sai dai sun ce sun gano dalilan da suka sa take kama wasu nau'ukan mata fiye da wasu.