Shirin 'Lafiya Jari ce' ya mayar da haankali ne a kan yadda mutane ke boye cutukan da ke damunsu har su kai ga ta'azzara a jikinsu, musammam cutukan da suka shafi kwakwalwa. sau da damu a cikin al'ummarmu, mutane ba sa zuwa ganin likitan kwakwalwa, ko kuma kaai 'yaan uwansu, don kawai kada a danganta su da laallurar tabin hankali.