Shirin Lafiya Jari Ce na wannan rana tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan karuwar matsalar ta'ammali da miyagun kwayoyi duk ikirarin mahukunta na yakar matsalar a matakai daban-daban, dai dai lokacin da wani binciken masana ke alakanta matsalar ta shaye-shaye da karuwar masu tabin hankalin da ake gani a sassan kasar.