Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Bashir Ibrahim Idris ya dora kan shirin makon jiya game da fasahar da wani matashi ya samar mai yanayi da dandalin sada zumunta na Watsapp wanda ya yiwa suna da Tabarau, da ke zuwa dai dai lokacin da aka samu daukewar kafofin sada zumunta na Watsapp, Facebook da kuma Instagram.