Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya maida da hankali ne kan karancin tsabar kudi a hannun ‘yan Najeriya sakamakon wa’adin daina amfani da wasu takardun kudin kasar Naira da babban bankin kasar CBN ya sauyawa fasali, lamarin da yasa wasu yankunan kan iyakokin kasar suka fara amfani da takardun kudin CFA.