Gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu, ta ce za ta ciyo bashin dala bilyan daya da milyan 500 domin cike gibin kasafin kudin kasar na shekara ta 2024 da ke tafe. Wannan yunkuri na shugaba Tinubu, ya yi hannun riga da alkawarin da ya yi kwanaki kadan bayan da ya karbi ragamar mulki, inda yake cewa shi kam, ba zai riko ciyo zunzuruntun bashi don gudanar da ayyuka kamar dai yadda gwamnatin da ta gabata ce shi ta rika yi.