Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan mako ya duba batun gasar kwallon kafa ta zakarun nahiyar Turai, wadda kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta Spain da Liverpool ta Ingila suka kai matakin wasan karshe, abin da nufin cewa kungiyoyin biyun za su barje gumi a wasan karshe na gasar. Shirin ya tattauna yadda wasannin kusa da karshe suka kaya tare da sharhi a kan karon battan da za a yi a wasan karshe.