
Sign up to save your podcasts
Or


Shirin Al’adun mu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya tabo batun kyautar da matashiya 'yan Farsans ta lashe, inda ta zamo ta daya a duniya a wannan shekarar wajen iya gasa biridi. Tarihi dai ya nuna wannan ne karo na faro da mace ta taba lashe wannan kyauta.
Haka nan, shirin ya kuma tattauna da masu ruwa da tsaki a bangaren kan wannan al'amari.
Ku danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin........
Shirin al'adunmu na gado na wannan mako ya duba wani babban taron kasa da kasa da aka gudanar kan habbaka harshen Kanuri da al'adunsa a jihar Kano da ke arewacin Najeriya
Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdoullaye Issa
Shirin Al'adunmu na wannan mako ya yada zango ne Masarautar Zazzau Suleja ta jihar Neja dake Najeriya domin shaida bikin murnar cika shekaru 30 na Sarkin Masarautar mai dimbin tarihi, Mallam Muhammadu Auwal Ibrahim, wanda ya kasance gwamnan jihar na farko na farar hula a jamhuriya ta biyu daga shekarar alif 979 zuwa alif 983.
Shirin Al’adun mu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon ya yi duba ne kan sana’ar wanzanci, wacce ke cikin sana'oin gargajiya na Hausawa da ke cike da abubuwa na al’ajabi. Mafi yawancin wanzamai gadon sana’ar suke yi daga iyayensu, amma wani lokacin, ana samun wasu daga waje da suke sha’awar koyon sana’ar don su samu hanyar cin abici. Duk kuwa da yadda bincike ya nuna cewa sana’ar ba abar da mutum zai koya cikin sauki da sauri ba ce.
Sakamakon yanda ake samun sauyin zamani, yanzu wanzamai sun fara fuskantar kalubale na rashin tabbas a sana'arsu saboda fara bacewar sana’arsu.
Ku danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin........
Shirin ala'dun mu na gado na wannan mako zai mayar da hankali ne kan taron inganta harshen Hausa da aka shirya a jami'ar Ouagadougou da ke Burkian Faso
Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdoullaye Issa
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda kabilar Dukkawa na jihar Neja da ke tarayyar Najeriya suke gudanar da bukukuwan gargajiya na shekara-shekara.
Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdullahi Isa
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali ne kan bikin kidan Duma, guda cikin al'adun jihar Maradi da ke kokarin gushewa.
A wani kokari na dakile gushewar al'adu, gwamnatin jamhuriyyar Nijar ta kaddamar da wani gangamin horar da matasa kidan Duma, salon kidan da ke da shahara a tsakanin garuruwan Hausawa.
Akwai dai salo kala kala na kidin Duma da yanzu ke zama inda mata sun fi son gargajiya yayin bukukuwansu abin da ake kira Partyn kauyawa Tasi’u Bakwai ya mana filla filla ma’anar kidi irinsu adamulmula, yar sahabi da sauransu.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin..............
Shirin 'Al'adunmu na Gado' na wannan makon zai duba yadda aka gudanar ad bikin doya na shekara-shekara a Jamhuriyar Benin. Ana gudanar da wannan biki na doya a duk shekara musaman a ranar 15 ga watan Agusta a garin Savalou dake Jamhuriyar Benin. Tun asali dai daya daga cikin kabilun yankin da aka sani da kabilar Salman ne ke shirya wannan bikin na gargajiya domin nuna godiya da samun damuna mai albarka.
Shirin Al'adunmu Na Gado na wannan maako ya kawo batutuwa da dama da suka hada da irin dangantakar da ke tsakanin kabilun arewacin Najeriya da na kudancin kasar. Mazauna arewacin Najeriya da akasarinsu yan kasuwa ne,na gudanar da harakokinsu na kai da kawo daga wani yankin zuwa wanin yankin daban,to sai dai wasusu a maimakon fatauci,ba sun rungumi almajiranci da iya sani da suke da shi da nufin korewa bakin kuda ta hanyar zuwa kudancin kasar a wancan lokaci.
Kamar dai yada muka saba a cikin Shirin za mu dubo halakar da ke tsakanin babar-bare da batun da ya shafi amfani da turare.
Bayan haka shirin ya duba yadda auren kabilar Tubawa yake a al'adance.
From the publisher's feed
Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin…

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners