A farkon wannan makon wani rahoton ƙwararru ya bayyana cewar, yawan albarkatun noma da ake fitarwa daga Najeriya zuwa ƙetare ya ragu da aƙalla kaso 31 cikin 100, sakamakon yadda ƙasashe musamman na Turai da Asiya ke ƙin karɓar kayayyakin abincin, ciki har da Wake da Zoɓo da dai sauransu.Rahoton ya bayyana amfani da magungunan kashe ƙwari fiye da kima, a matsayin ɗaya daga cikin dalilan da ke kan gaba wajen janyowa Najeriya wannan hasara.
Maudu'in da masu sauraro suka tofa albarkacin bakinsu akai kenan.