Sanata Natasha Uduaghan ta shigar da ƙorafi a hukumance tana zargin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Godswill Akpabio da neman yin lalata da ita, yayin da nan take wata kotu a Abuja ta fitar da huukuncin hana yin bincike game da wannan batu har sai ta kammala nata binciken.
Tuni dai zargi ya haifar cece-kuce a tsakanin ƴan Najeriya, yayin da wasu ke ganin cewa dole ne a binciki wannan zargi saboda yadda yake neman shafar ƙimar kujerar da Sanata Akpabio ke zaune a kanta.
Za ku iya bayyana ra’ayoyinku a game da wannan batu akan lambarmu ta Whatsapp da kuma shafinmu na facebook.