Yayin da ake ci gaba da rokon Allah sakamakon fari a wasu jihoji na Najeriya, a wasu yankuna kuwa, ana ci gaba da samun ambaliya wadda ke haddasa mummunar barna har ma da asarar rayuka.
Matsalar dai ta fi yin kamari ne a arewacin Najeriya, kamar dai yadda tuni ambaliyar ta afka wa wasu yankuna na Jamhuriyar Nijar.
Shin kowane hali ake ciki a yankunanku?
Wadannan matakai ku ke dauka domin rage illolin wannan ambaliya?