Shirin Dandalin Fasahar Fina-finai ya yi tattaki zuwa Katsina don tattaunawa da mawaki, Boda a kan wakar gamayya ta Ramadan, kana ya leka masana'antar frina-finai ta kudancin Najeriya, Nollywood don jin wainar da ake toyawa danagane da zargin da ake wa wani jarumin masana'antar na cin zarafin wata karamar yarinya.
A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina - Fiinai, Hausa Kabir ta yi hira da mawakin Hausa, Abba Don , wanda ya jagoranci hadakar mawaka wajen raira wakar azumin wata Ramadan. A yi sauraro lafiya.
Shirin Dandalin Fasahar Fina-finai na wannan makon ya cika da tattaunawa da masu ruwa da tsaki akan matsalolin dake kunno kai tsakanin masu shirya fina-finai da kuma taurari.
A cikin wannan shiri na 'Dandalin fasahar Fina-Finai', Hauwa Kabir ta tattauna da babban tauraro a masana'antar Kannywood ta fina-finan Hausa Alhaji Tahir Fagge, inda ya yi bayani a ka gwagwarmayar rayuwa da irin kalubalen da suka addabi sana'arsa. Hauwa ta kuma duba masana'antar fina-finan Yarabawa a kudancin Najeriya.
A Najeriya,yan wasan Fim da dama ne yanzu ke sa ran ganin sun samu zama tareda kasancewa jarumai a Duniyar Nollywood gida dama wajen kasar.
Hawa Kabir ta samu tattaunawa da daya daga cikin yan wasan Fim mai suna Zuwaira,banda haka ta kuma duba wasu daga cikin matsalollin da yan wasan na Fim ke fuskanta a wannan Duniya.
Hauwa Kabir ta tattauna da jarumar Kannywood, Saratu Abubakar Zazzau a kan daukakar da ta samu a fagen fina - finai bayan shekaru 21 a cikin masana'antar, da dai sauran abubuwa a cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina- Finai.
A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai', Hauwa Kabir ta duba wasu daga cikin abubuwan da suke wakana a fannin fina finai da wakoki, ciki har da zanga - zangar da wasu masoyan mawaki Nura M. Inuwa suka yi sabili da dadewa da ya yi bai saki waka ba.
A cikin shirin fina-finai,Hawa Kabir ta samu zantawa da masu shirya Fim a Najeriya,domin jin ko a ina aka kwana dangane da batun shirya fim a kasar,yanayin rayuwar yan Fim a Najeriya.
Hama Kabir ta dubo wasu daga cikin labaran da suka shafi Duniyar yan Fim a Indiya a cikin wannan shirin na Dandalin fasahar fina-finai.
Shirin Dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon ya cigaba da tattaunawa da shugaban hukumar tace fim na jihar Kano kan wasu muhimman al'amuran da suka danganci masa'antar
.
21 min
About Dandalin Fasahar Fina-finai
From the publisher's feed
Fili ne na musamman kan Fina-finai ta hanyar tattauna da masu ruwa da tsaki a wannan fanni a duniya, Tare da wayar wa ma su sauraro kai da kara masu basira dangane da hikimar da Allah ya bai wa…
wasu ta fanin shirya fim ko tsara wasan kwaikwayo. Wanda ke zo maku a duk ranar Asabar da safe, tare da maimaici a ranar Lahadi da yamma.