
Sign up to save your podcasts
Or


Shirin Lafiya Jari ce na wannan mako ya yi dubi ne kan yawaitar cututtuka a irin wannan lokaci na damuna, daidai lokacin da bayanai ke nuni da cewa farashin magunguna ya yi tashin gauron zabbi.
Latsa alamar sauti don sauraren shirin tare da Azima Bashir Aminu...
Shirin a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan nasarar da jihar Kano ke iƙirarin samu bayan fitar wani rahoto da ke cewa an samu raguwar mace-macen mata a lokacin haihuwa a sassan jihar wadda a baya ke sahun gaba wajen asarar rayukan ɗimbin mata a lokacin haihuwa ko goyon ciki
Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin..........
Shirin Lafiya Jari Ce a wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan cutar ƙaba ko ƙarin mahaifi ko kuma fibroids da ke addabar tarin mata ta yadda da dama ke rayuwa da shi ba tare da sani ba, yayinda wanzuwarsa a mahaifa kan haddasa matsala ga yanayin haihuwa ga matan.
Galibi mata a tsakanin shekaru 35 zuwa 37 ne suka fi kamuwa da wannan lalura ta Fibroids, a wani yanayi da ƙididdiga ke cewa kaso mai yawa na mata na fara gamuwa da ɓirɓishin lalurar ne tun daga lokacin da suka haura shekaru 20 a duniya.
A baya-bayan nan ana yawan ganin matan da ke ƙorafi kan lalurar ta Fibroids ko kuma ƙarin mahaifa.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin na Lafiya Jari ce zai a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan zazzaɓin Typhoid, cuta mai haɗari wadda ƙwayar cutar Salmonella Typhi ke haddasawa, inda ta kan yaɗu ta hanyar abinci ko ruwan da ya gurɓata.
Danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......
A wannan makon shirin ya yi duba ne kan ƙaruwar masu fama da cutar sikila a jamhuriyyar Kamaru bayan fitar wani rahoto da ke cewa cikin shekara 1 kaɗai an tattara alƙaluman sabbin mutum dubu 6 da aka gano suna ɗauke da cutar.
Wannan cuta mai alaƙa da nau’in jini, na daga cikin matakan yaƙi da ita shi ne tabbatar da gwaje-gwajen jini tun kafin aure don kaucewa haifar yara masu ɗauke da ita, ganin cewa hanya ɗaya tal ta samun masu cutar shi ne ta hanyar gado wato daga iyaye.
Shirin lafiya Jari ce a wannan makon ya mayar da hankali kan yadda mata suka rungumi tsarin gyaran jiki ta fannoni daban-daban kama daga magungunan sha ko mayukan shafawa ko kuma salon amfani da na’ura da nufin ƙawata sura.
Wasu daga cikin batutuwa mafi jan hankali a wannan babi na gyaran jiki shi ne tayar da komaɗar fata da sauran sassan jiki don killacewa ko kuma kange kai daga bayyanar tsufa, kuma guda cikin tsarin da ake amfani da shi shi ne na’urorin zamani wanda ƙwararru a wannan fanni na fata gashi da kuma ƙumba ke cewa kafin yanzu abin bai samu karɓuwa a Najeriya ba.
Shirin a wannan mako zai ɗora ne akan wanda ya gabace shi a makon jiya, sai dai a wannan karon zamu karkata ga illolin da magungunan matsi ke haifarwa ga lafiyar mata, duk da ya ke matan kan yi don bajinta ko nuna isa a wajen mazajensu.
Danna alamar sauti don sauraron karin bayani.....
Shirin Lafiya Jari ce na wannan makon ya yi nazari kan ƙaruwar matan da ke fama da cutuka masu alaƙa da al’aura ko kuma matantaka, tare da laluben hanyoyin magancesu ta hanyar tattaunawa da ƙwararru a wannan fanni, cutukan da ƙwararrun ke alaƙantawa da rashin baiwa al’aurar kariya wanda a lokuta da dama ke haddasa gagarumar matsala.
Ku lasha alamar sauti don sauraron shirin tare da Azima Bashir Aminu...........
Shirin Lafiya Jari Ce a wannan makon ya yi nazari kan cutar Hantavirus da duniya ta ga ɓullarta a baya-bayan nan, lamarin da ya sanya fargaba a zuƙatan jama’a, musamman ganin yadda ake alaƙanta wannan cuta a sahun masu haɗari da tarihi ya nuna yaddda suka yiwa duniya ɓarna matuƙa.
Cikin watan jiya ne aka ga ɓullar wannan cuta a wani jirgi da ya taso daga Argentina zuwa Cape Verde, sai dai tilas ya samu izinin yada zango a tsibirin Spain sakamakon yadda cutar ta kashe mutane 3 ta kuma harbu wasu mutum 8.
Duk da cewa Majalisar ɗinkin duniya ta nesanta alaƙar wannan cuta ta Hantavirus da kasancewa covid-19 ta biyu amma mutane na cike da fargaba.
Ku latsa alamar sauti don sauraron ciakken shirin tare Azima Bashir Aminu........
Shirin lafiya jari Ce a wannan makon zai nazarci yadda ake gudanar aikin yaki da cutar polio tsakanin ƙasashen makwabtan juna wato Najeriya da Nijar a wani yunƙuri na kakkaɓe ɓurɓushin wannan cuta musamman a yankunan kan iyaka na ƙasashen biyu duk kuwa da saɓanin diflomasiyyar da ke tsakanin gwamnatocin ƙasashen biyu.
From the publisher's feed
Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi,…

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners