
Sign up to save your podcasts
Or


Shirin lafiya jari ce na wannan mao ya mayar da hankali ne kan wani rahoto da ke cewa mutane akalla miliyan 24 ne ke fama da cutar Suga a Nahiyar Afrika kawai.
Wannan kuwa na faruwa ne a dai-dai lokacin da cutar ke sauya salo da tsanani ga masu fama da ita, baya ga bijirewa magani.
Danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.
A wannan makon shirin Lafiya jari ce ya mayar da hankali kan wani bincike a Ghana da ke nuna yadda mutane sama da dubu 28 ke mutuwa duk shekara saboda gurbacewar iska.
Alƙaluman hukumar kula da Lafiya ta Ghana ne ke sanar da wannan adadi, wanda kai tsaye ke nufin duk mintuna 19 wannan matsala ta gurɓatacciyar iska kan sabbaba mutuwar mutum guda a wannan ƙasa ta yammacin Afrika, batun da ke buƙatar kulawar gaggawa don ɗaukar matakan da suka dace.
Latsa alamar sauti don sauraren shirin tare da Azima Bashir Aminu...
Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako ya mayar da hankali kan alaƙar cutar yunwa da kuma lafiyar ƙwaƙwalwa, inda a cikin shirin zakuji yadda masana a ɓangaren suka alakantawa waɗannan matsaloli biyu a matsayin lalurori masu tafiya kafaɗa da kafaɗa da juna.
A kowacce ranar 10 ga watan Oktoba ne duniya ke gudanar da gangamin kula lafiyar ƙwaƙwalwa don bikin ranar ta lafiya ƙwaƙalwa ko kuma World Mental Health Day a turance, da nufin wayar da kai game da muhimmancin lafiyar ƙwaƙwalwa dama matsalolin da ka iya barazana ga ƙwaƙalwa, sai dai a wannan karon ƙungiyar likitocin ƙasa da ƙasa ta MSF ta alaƙanta ƙarancin abincin mai gina jiki da ke haddasa cutar da yunwa da matsalar ƙwaƙwalwa...... wannan shi ne maudu’in da shirin Lafiya Jari ce na wannan mako zai mayar da hankali akai, sai ku biyo mu....
Wani rahoto da MSF ta fitar a ranar ta 10 ga wata ta koka da ƙaruwar yaran da ke fama da cutar yunwa sakamakon ƙarancin abinci mai gina jiki, wanda ta ce matsala ce kai tsaye da ke shafar lafiyar ƙwaƙwalwa.
Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.
Kowanne watan Oktoba, lokaci ne da ɓangarorin lafiya a Jamhuriyyar Nijar ke amfani da shi wajen gudanar da gangamin wayar da kai a ƙasa baki ɗaya game da cutar sankara ko kuma Cancer wadda ake ganin ƙaruwar masu kamuwa da ita a sassan wannan ƙasa ta yankin Sahel,,,, wannan shi ne maudu’in da shirin na Lafiya jari ce zai mayar da hankali akai sai ku biyomu.
Jamhuriyyar Nijar na ganin sabbin kamuwa da cutar ta cancer dubu 9 da 787 duk shekara ciki kuwa har da mata masu kamuwa sankarar mama dubu 2, wanda ke matsayin wani ɓangare na jumullar mata miliyan 2 da dubu 300 da ke kamuwa da sanakarar maman duk shekara a sassan duniya bisa alƙaluman hukumar WHO.
Shirin a wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba kan yawaitar samun cutar Kwalara ko kuma amai da gudawa a sassan Najeriya, cutar da a baya-bayan nan ta kashe ɗimbin al'umma a ƙasar mafi yawan jama'a a Nahiyar Afrika. Wasu alƙaluma da hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta ƙasar NCDC ta fitar sun nuna cewa mutane kimanin dubu biyar (5,000) cutar ta kwalara ta halaka a sassan Najeriyar daga shekarar 2020 zuwa 2025 da muke ciki.
Latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Azima Bashir Aminu.............
Shirin a wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba kan ciwon hanta nau’in B ko kuma Hepatitis B a turanci, cutar da masana ke gargaɗi game da yadda ta ke yaɗuwa kamar wutar daji tsakanin jama’a.
Wasu alƙaluma sun nuna yadda ake da mutum fiye da miliyan 257 da ke fama da wannan cutar, a wani yanayi da Najeriya ke sahun ƙasashe 5 masu ɗauke da kashi 60 na masu wannan cuta a duniya baki ɗaya.
Masana a ɓangaren lafiyar Najeriya sun bayyana yadda wannan cuta ta Hepatitis B ke yaɗuwa kamar wutar daji a sassan ƙasar, kuma abin dubawar shi ne yadda mutane da yawa ke rayuwa da cutar yanzu haka ba tare da sanin suna ɗauke da ita ba, kan hakan kuma muka nemi ji daga masana irin Dr Misbahu Sahabi na Cibiyar Kiwon Lafiya ta tarayya da ke garin Birnin Kudun jihar Jigawa, wanda ke cewa tun farko cutar na da rabe-rabe wato mai haɗari da kuma mai sassaucin illa.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin Lafiya Jari Ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali yadda wasu alƙaluman baya-bayan nan a jihar Kaduna ta Najeriya ke nuna yadda ake samun ƙaruwar matan da ke mutuwa yayin goyon ciki ko haihuwa, wanda ke da nasaba da yadda jama’a ke ƙauracewa asibitoci walau a lokacin awo ko kuma haihuwa, wannan shi ne maudu’inmu na wannan mako sai ku biyomu.
Wani binciken baya-bayan nan ya gano cewa matsalar ta mace-macen mata masu juna biyun tafi ta’azzara a ƙananan hukumomin jihar ta Kaduna guda 7 ciki har da Zaria.
Ɗimbin mata ne ke kafa hujja da halin rayuwa a matsayin dalilin da ke nesantasu da asibiti a lokacin goyon ciki ko haihuwa, kodayake masana na ganin babu wani dalili na ƙin kai mai juna asibiti, tare da zuba mata ido musamman idan haihuwa ta zo da tirjiya, sai dai wasu bayanai na cewa gwamnatoci a matakai daban-daban na sauƙaƙa tsarin karɓar haihuwar musamman ga marasa ƙarfi.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin na Lafiya Jari ce a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan yadda ake ganin yawaitar jinyace-jinyace mabanbanta da kan kwantar da jama’a kama daga mashasshara ko mura ko kuma ƙurajen jiki dama wasu nau’in cutukan daban-daban, musamman ga ƙananan yara a lokacin damuna.
Zubar ruwan sama da yawaitar ƙwari baya ga raɓa na daga cikin abubuwan da kan haddasa cutukan dama ƙamjiki, batun da Dokta Ila Aishatou jagorar gidan asibiti CSI stade a birnin Damagaram ke cewa akwai matakai na kare kai daga irin cutukan na damuna musamman ga ƙananan yara.
Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.
Shirin Lafiya Jari ce na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu, ya maida hankali ne kan yadda jama’a suka fi yadda da shagunan sayar da magunguna na bakin titi wato Chemist, maimakon zuwa asibiti domin ganin Likita.....
Latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin..........
Shirin lafiya jari ce a wannan mako ya leƙa Jamhuriyar Nijar, inda a dai dai lokacin da ake ganin yawaitar ƙananan yaran da ke fama da cutar yunwa sanadiyyar ƙarancin abinci mai gina jiki da ake kira ƙwamuso a sassan jamhuriyar Nijar, wata matsala da ke tunƙaro shirin yaƙi ko kuma taimakon masu fama da lalurar shi ne yadda ake karkatar da abincin da aka tanadar dominsu.............
From the publisher's feed
Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi,…

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners