
Sign up to save your podcasts
Or


Shirin Lafiya Jari Ce a wannan makon shirin ya mayar da hankali kan yadda wani bincike ke gano cewa yawan shan suger ko kuma sikari a lokutan ƙuriciya na taka muhimmiyar rawa wajen haddasawa mutum ciwon suga a lokacin girma. Wannan cuta ta suga ko kuma Diebetes na cikin jerin cutukan da ke barazana ga rayukan ɗimbin mutane musamman a sassan Najeriya da tuni cutar ta fara zama ruwan dare mai gama duniya.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu............
Shirin 'Lafiya Jari Ce na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan hasashen da wata ƙungiya ta yi cewar nan da shekarar 2025 raɓin al'ummar Afirka masamman matasa za su fuskanci cutar ƙibar da ta wuce ƙima ko Obesity a turance.
Shirin namu na wannan makon zai mayar da hankali ne kan ƙaruwar mutanen da ke kamauwa da cutar babban tari, ko kuma tarin fuka, ko kuma TB a sassan Jamhuriyar Nijar, lamarin da ke zuwa a lokacin da ake fuskantar ƙarancin agajin magangunan yaƙi da wannan cuta. Wanmnan cuta na sahun daɗaɗɗun cutuka masu yaɗuwa, waɗanda wani kan iya goga wa wani.Abin da ya sa ya zama wajibi a rika wayar da kan al'umma akan hanyoyin kariya daga ita.
Shirin Lafiya jari ce a wannan makon ya yi duba na musamman game da dawowar cutar Polio a Najeriya, cutar da alamu ke nuna nasarar yaƙarta ke yiwa ƙasar kwan gaba kwan baya, lura da yadda a lokuta da dama ake sake ganin ɓullarta bayan nasarar kawar da ita, kodayake ƙwararru sun ce wadda ta ɓulla a wannan karon ba wadda aka saba gani ba ce kuma bata kai waɗanda suka gabace ta illa ba.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu............
Shirin Lafiya Jari ce na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan shaushawar ƙyandar da mahukuntan Jamhuriyar Nijar suka jagoranta sakamakon ɓullar cutar wadda a duk lokacin da aka ga bazuwarta ta ke yiwa ƙananan yara illa matuƙa.
Dai dai lokacin da duniya ta gudanar bikin makon rigakafi a ƙarshen watan Mayun da ya gabata, a Jamhuriyyar Nijar annobar ƙyanda ce ke ci gaba da yaɗuwa tare da galabaitar da ɗimbin ƙananan yara, lamarin da ya tilasta mahukunta ɗaukar matakan yiwa jama’a rigakafin wannan cuta mai haɗari.
Cutar ta Ƙyanda ko Ado ko kuma Dusa na matsayin babbar matsalar kiwon lafiya ta yadda a duk lokacin da ta ɓulla ta kan haddasa asarar ɗimbin rayuka, kodayake a yanzu tuni ma’aikatar lafiya ta jagoranci aikin rigakafin na ƙasa baki ɗaya da zai shafi dukkanin ƙananan yara tun daga watanni 6 da haihuwa har zuwa shekarun 5 da nufin murƙushe cutar.
Tsawon mako guda aka shafe daga ranar 18 zuwa 24 ga watan Mayu ana gudanar da rigakafin na ƙyanda a sassan Nijar wanda aka yiwa ƙananan yaran da yawansu ya tasamma miliyon 5 a kasar, da nufin daƙile asarar rayukan da ake fuskanta sanadiyyar cutar.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin Lafiya Jari ce na wannan makon, ya mayar da hankali ne kan nau’ikan cutukan da ke bazuwa sakamakon cuɗanyar da jama’a ke yi wajen amfani da kayayyakin da bisa ƙa’ida yakamata kowanne mutum ya yi amfani da nasa shi kaɗai. Har yanzu ana samun waɗanda ke yin gamayya wajen amfani da moɗar-shan ruwa ko cokali ko kuma kwanon cin abinci dama sauran kayakin da basu cancanci amfanin gamayya ba, lura da yadda cikin sauƙi hakan ke iya yaɗa cutuka.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu........
Shirin Lafiya Jari ce a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan matakan da ya kamata mutane su riƙa ɗauka gabanin kai ɗaukin gaggawa a lokacin afkuwar haɗari ko ibtila'i, waɗanda rashinsu a wasu lokutan ke kaiwa ga asarar rayuka ko kuma haddasa gagarumar illa ga mutanen da haɗarin ya rutsa da su.
Shirin ya shawarci jama'a game da samun ilimin iya kai ɗaukin gaggawa don kaucewa haddasa matsala ba tare da sani ba ga mutanen da ake ƙoƙarin ceton rayuwarsu.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan ƙaruwar masu kamuwa da cuta mai karya garkuwar jiki ko kuma HIV AIDS ko sida tsakanin matasan Ghana a shekarun baya-bayan nan, wadda masana ke ɗora alhakin yawaitarta kan rashin ɗaukar matakai.
Wannan ƙaruwar alƙaluma na zuwa a dai dai lokacin da duniya ke ganin ƙarancin magunguna rage kaifin cutar sakamakon matakin Amurka na zaftare tallafin da ta ke bayarwa ƙarƙashin ƙungiyar USAID.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shiri.
Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya yi duba na musamman kan cutuka ko kuma lalurar ƙwaƙwalwa, dama rabe-rabenta baya ga nazarin yadda mutane ke ɓoye irin wannan lalura saboda kunyar kar a alaƙanta su da ciwon hauka.
Alƙaluman hukumar lafiya ta duniya WHO a shekarar 2017 sun nuna cewa kashi 19 na yawan al’ummar duniya na fama da matsalar ƙwaƙwalwa walau a babban mataki ko kuma a mataki na ƙasa, matsalar da kuma bayanan hukumar ke cewa yafi tsananta a ƙasashe masu tasowa.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon ya mayar da hankali ne akan cutar sankarau, wanda ke yin ƙamari a cikin yanayi na zafi da ake ciki, musamma a ƙasashenmu na nahiyar Afrika. Tuni aka samu ɓullar cutar sankarau a sassa daban-daban na Najeriya inda ta kashe gomman mutane a jihohin Kebbi da Sokoto, wadda aka bayyana ta da annoba.
Masana a ɓangarorin lafiya da kuma yanayi, na ci gaba da gargaɗi kan yiwuwar ɓullar tarin cutuka sakamakon tsananin zafin da ake fuskanta a wasu daga cikin jihohin Najeriya, a wani yanayi da ake ci gaba da azumin watan Ramadana,, wannan shi ne maudu’in da shirin lafiya jari ce na wannan mako zai mayar da hankali akai sai ku biyomu.
From the publisher's feed
Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi,…

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners