
Sign up to save your podcasts
Or


A wannan makon shirin na lafiya jari ce ya mayar da hankali kan cutar kuturta ko kuma Lebrosy ko albaras, cutar da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ke ganin sam bai kamata a samu ɓirɓishinta a banƙasa ba.
Rayuwar masu wannan lalura ta kuturta rayuwa ce mai cike da ban tausai, musamman waɗanda ke killace a asibitin na Bela wanda Turawan mishan daga Netherlands suka samar tun a shekarar 1928 wato tun gomman shekaru kafin ƴancin Najeriya.
Alƙaluma sun nuna cewa, duk shekara Najeriya na ganin fiye da mutum dubu guda sabbin kamuwa da wannan cuta ta kuturta wadda tuni ta zama tarihi a wasu sassa na duniya.
Masu lalurar ta kuturta na rayuwa cikin yanayi na tsangwama ko ƙyama wannan dalili ya sanya da dama daga cikinsu tattarewa a Bela.
Shirin ''Lafiya Jari Ce'' tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon, ya kai ziyara wasu asibitocin yankunan karkara a arewacin Najeriya, inda sashen Hausa na RFI ya ganewa idonsa tarin matsalolin da suka dabaibaye irin waɗannan asibitoci da bisa al’ada ke matsayin masu kula da lafiya a matakin farko.
Tarin asibitocin yankunan karkarar jihar Kano na fama da matsaloli kama daga rashin malaman jinya da kuma rashin wadatattun kayakin aiki, koma rashin ginin Asibitin ɗungurugum, ta yadda da dama daga cikinsu suka juye daga matsayin cibiyoyin kula da lafiya zuwa dandalin shaƙatawar dabbobi.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin Lafiya jari ce a wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan yadda fasahar cire ɗa ta hanyar CS ke taimakawa wajen ceto rayukan uwa da ɗa da nufin rage asarar rayukan da ake fuskanta a lokacin haihuwa.
Duk da cewa haihuwa 3 cikin 100 ce kaɗai ake yi ta hanyar tiyata ko kuma CS a Najeriya bisa alƙaluman 2019, amma a baya-bayan nan ana ganin yawaitar matan da ake yiwa CS gabanin haihuwa kama daga nau'in matan da basa zuwa asibiti da kuma mata masu shekaru da yawa ko waɗanda suka yi haihuwa da dama, duk dai a ƙoƙarin kange yawaitar mace-macen mata ko kuma asarar jariran da ake gani a sassan ƙasar mafi yawan jama'a a nahiyar Afrika.
Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.
Shirin ''Lafiya Jari Ce'' tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako ya yi duba ne kan matakin gwamnatin Najeriya na tsawaita lokacin ritayar likitoci da malaman jinya a wani yunƙuri na ganin sun ci gaba da bayar da gudunmawa ga al’ummar wannan ƙasa wadda ke fama da ƙarancin ƙwararrun likitoci.
Matakin na gwamnatin Najeriya ya nuna cewa Likitocin ko kuma sauran jami’an lafiya na da zaɓin ƙarin shekaru 5 akan ainahin shekarunsu na ritaya, ta yadda za su kai har shekaru 65 na haihuwa a bakin aiki maimakon shekaru 60 a baya, ko da ya ke wannan mataki bai samu maraba daga wasu unguzoma ba.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin....
Shirin ''Lafiya Jari ce'' tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako ya yi duba ne kan matsalar rashin zuwa awo da ke matsayin babban ƙalubalen ga mata masu juna biyu a yayin goyon ciki ko kuma haihuwa, matsalar da aka fi ganin ta’azzararta a yankunan karkara, wadda a lokuta da dama ke kaiwa ga asarar rayukan walau uwa ko jariri.
Ƙorafe-ƙorafen jami’an lafiya na ci gaba da yawaita kan matsalolin da suka dabaibaye tsarin renon ciki da kuma haihuwa a yankunan karkara, matsalar da wala’alla ake ganin ta na da alaƙa ta ƙut da ƙut da halin matsi ko kuma tsadar rayuwar da ake fama da ita wadda ta ƙai ƙololuwa a yankin arewacin Najeriya mai fama da durƙushewar ɓangaren kiwon lafiya.
Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.
Shirin lafiya Jari ce na wannan makon ya taɓo batun yadda kwararrun likitoci ke tserewa daga Najeriya, inda wasu alkaluma suka nuna cewa a cikin shekaru biyar da suka gabata, sama da likitoci dubu 16 suka fice daga ƙasar don yin aiki a wasu ƙasashen ketare, lamarin da ke barazana ga tsarin kula da lafiya a ƙasar.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu............
Shirin Lafiya jari ce bisa al'ada tare da Azima Bashir Aminu na yin duba ne kan wasu batutuwa da suka shafi kiwon lafiya, kuma a wannan makon ya yada zango a Jamhuriyyar Nijar inda wasu ƙungiyoyin agaji suka yiwa tarin mutanen da ke fama da matsalar cutar yanar ido aiki a ƙokarin dawo musu da ganinsu.
A cikin shirin za ku ji yadda kusan kashi 2 cikin 100 na al'ummar wannan ƙasa ta yankin Sahel ke fama da matsalar lalurar ta yanar ido a wani yanayi da mahukunta tare da taimakon ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa ke fatan magance matsalar zuwa ƙasa da kashi 1 nan yan shekaru masu zuwa.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu bisa al’ada kan taɓo batutuwan da suka shafi kiwon lafiya ko kuma a lokuta da dama ya lalubo ƙalubalen da fannin lafiyar ke fuskanta don ankarar da mahukunta da nufin ɗaukar matakan gyara.
A wannan makon shirin na Lafiya Jari ce ya mayar da hankali kan tazara ko kuma tsarin iyali ko Family Planning wanda ke sahun shawarwarin kiwon lafiya da ke ganin kakkausar suka musamman a arewacin Najeriya wala’alla saboda yadda tsarin ya ci karo da al’adun al’ummomin wannan yanki, sai dai a baya-bayan nan alamu na nuna yadda wannan tsari ke samun karɓuwa gadan-gadan.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin....
A wannan makon shirin na lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan yadda aka samu ɓarkewar cutar sankarau a wata Makaranta da ke jihar Maradin Jamhuriyar Nijar, cutar da tuni ta harbi tarin ɗalibai, a wani yanayi da masana ke gargaɗi kan haɗarin da ke tattare da wannan cuta musamman nau’in wadda ake ganin ɓullarta a lokacin sanyi.
Kafin yanzu akan ga ɓullar cutar sanƙarau ne a lokaci na zafi sai dai a shekarun baya-bayan nan ana ganin yadda wannan cuta kan sauya salo tare da ta’azzara a lokacin sanyi wadda masana ke ganin ta na da haɗari matuƙa a wasu lokutan illarta kan zarta wadda ake ganin ɓullarta a lokacin sanyi, kasancewarta mai saurin kisa matuƙar ba a ɗauki matakan gaggawa ba.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin..............
Shirin lafiya jari ce na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda lokacin sanyi ko kuma hunturu kan zo da wasu keɓantattu ko kuma tayar da wasu kwantattun cutuka. Nau’ikan cutukan da suke barazana ko kuma tashi a irin wannan lokaci na hunturu sun ƙunshi mura ko tari, ko ciwon hakori baya ga saɓar fata kana yawan fitsari ko cutuka masu alaƙa da zuciya yayinda cutuka irin sikila ko asma kan tashi duk dai a wannan lokaci.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.......
From the publisher's feed
Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi,…

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners