
Sign up to save your podcasts
Or


Shirin lafiya jari ce a wannan makon ya mayar da hankali ne game da matsalar zuƙar taba sigari a cikin al'umma saɓanin wasu keɓantattun wurare da doka ta tanada. Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce a duk shekara sama da mutane miliyan 8 ne ke mutuwa sanadiyar shakar hayakin taba sigari kuma daga cikin wancan adadi, akwai sama da yara dubu 65 waɗanda lamarin ke shafa.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....
Shirin lafiya jari ce a wannan makon ya mayar da hankali kan yadda ake ganin ƙaruwar masu fama da cutar amasonin jini, ko Sickler ko kuma Emasi, batun da ke da alaƙa ta kai tsaye da auratayyar da ake yi tsakanin masu nau’ikan jinin da masana ke gargaɗi kan illar da hakan ke da shi ga ƴaƴan da za su haifa.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....
A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan abubuwan da ke haddasa cutar koda, la'akari da yadda cutar ke tsananta a wannan lokaci musamman a kasashe irin Najeriya, sabanin a lokutan baya da ba kasafai ake ganinta ba, baya ga karancin wuraren wankin kodar da ake fama dasu wato dialysis centers a turance.
Wani bincike na baya-bayan nan na nuni da cewa cutar koda ita ce ta 10 cikin cututtukan da ke kan gaba wajen haddasa mace-mace a fadin duniya, inda binciken ya nuna cewa kuma tana shafar kusan kashi 10 na al'ummar duniya, wanda a halin yanzu sama da mutane miliyan 850 ke fama da ita.
Shirin lafiya jarice na wannan mako ya mayar da hankali ne kan cutar katsewar laka wacce ke iya afkuwa a sanadiyar hadarin mota ko makamantansu da rikice-rikice ko fadowa daga wurare masu tudu da dai sauransu.
Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin
A wannan mako shirin zai mayar da hankali game da cuta ko kuma ‘‘lalurar katsewar Laka’’ wato Spinal cord Injury, lalurar da a baya-bayan nan alƙaluma ke nuna yawaitar masu fama da ita a sassan Najeriya, walau sakamakon haɗarin mota ko rikici dama sauran dalilai.
Yayin bikin ranar wayar da kai game da lalurar ta Laka da ke gudana a kowanne wata na Satumba, da a wannan karon aka yiwa take da ‘‘ Kawar da tarzoma a matsayin hanyar kawar da laka’’ masana sun ce baya ga haɗurran mota hanyoyi da dama na haddasa wannan lalura ta laka.
A wannan makon shirin zai mayar da hankali kan cutar borin gishiri ko kuma kumburin da mata ke fama da ita yayin da suke da dauke da juna biyu, wacce kuma a lokuta da dama kan haddasa asarar rayuka. Wannan cuta a Jamhuriyar Nijar na daga cikin wacce ke ciwa hukumomi tuwo a kwarya ganin yadda mata sama da dari biyar da 30 cikin kowace mace dubu daya ne kamuwa da wannan cuta, kuma sama da 50 ke rasa ransu a sanadiyarta.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....
A wannan makon shirin zai mayar da hankali kan ƙaruwar ƙananan yaran da ke fama da cutar yunwa ko kuma Tamowa a yankunan da ke fama da ƙarancin abinci, cikinsu kuwa har da Nijar, ƙasar da alƙaluman 2021 ke cewa akwai ƙananan yara ƴan ƙasa da shekaru 5 akalla miliyan 1 da dubu 800 da ke fama da rashin abinci mai gina jiki.
A baya-bayan nan anga ƙaruwar yaran da ke fama da cutar Tamowa ko da ya ke har yanzu akwai ƙaranci sani game da cutar, kan hakan mu ka fara da tuntuɓar Dr Fayuz Mu’azu likitan mai kula da ƙananan yara masu fama da cutar Tamowa a jihar Diffa, ya kuma yi mana bayani kan cutar da dalilan da ke haddasata.
Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon zai mayar da hankalli ne a kan gargaɗin da hukumar kiyaye ingancin abinci da magunguna a Najeriya, wato NAFDAC ta yi a kan hatsarin da ke tattare da amfani da maganin kashe ƙwari na Sniper a wajen adana kayan abinci domin kare su daga ƙwari. NAFDACdai ta jaddada haramcin da ta yi a kan amfani da wannan magani da ma sshigowa da shi Najeriya, bayan da ce bincikenta ya tabbatar da cewa maganin yana haddasa cutuka da suka haɗa da cancer.
Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya tattauna ne kan tasarin nau'ukan abinci da akan ƙirkira a ɗakunan bincike wadanda ake kira Synthetic foods a turance, domin nazari kan illolinsu ko kuma akasi ga lafiyar jama'a, duba da yadda nau'ukan abinci da nomansu akayi ba ko kiwo ke samun ƙarbuwa a wasu kasashen duniya.
Shirin Lafiya Jari ce na wannan mako ya yi duba ne kan yadda kansar bakin mahaifa ke hallaka Mata, musamman ƴan tsakanin shekaru 15 zuwa 44, a Najeriya.
Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron shirin...
From the publisher's feed
Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi,…

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners