Lafiya Jari ce

Lafiya Jari ce

By RFI Hausa
Download on the App Store

Lafiya Jari ce episodes

  • Har yanzu 'yan Najeriya da dama basa cin gajiyar shirin Inshorar lafiya -Bincike

    Shirin lafiya jari ce a wannan makon ya yi duba ne kan yadda har yanzu wasu daga cikin al’ummar Najeriya basa amfani da tsarin inshorar lafiya. A shekarar 2022 ne gwamnatin kasar ta sake dawo da dokar inshorar lafiya da aka samar tun 1999, a wani yunƙuri na sauƙaƙawa Jama’a samun kulawar lafiya cikin rahusa, lura da yadda kaso mai yawa na al’ummar ƙasar ke rasa kudaden iya kai kansu ga likitoci ko da suna cikin matsananciyar cuta. 

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu......

    10 min
  • Bayani a kan cutar ƙyanda da yadda za a kare yara daga kamuwa

    A wannan makon shirin zai yi duba kan cutar kyanda ko kuma measles a turance, cutar da galibi akan ga bullarta a irin wannan lokaci da ake fama da matsanancin zafi musamman a yankunan kasashen yammacin Afrika Sahel.

     

    Zuwa karshen watan Fabarairun da ya gabata, fiye da yara 700 suka harbu da cutar kyanda a jihar Borno cikin watan yayinda zuwa yanzu ta kashe kananan yara 42 a jihar Adamawa yayinda wasu fiye da dubu guda suka harbu.

    Bari mu bude da rahoton wakilinmu Ahmad Alhassan daga jihar Adamawa, jihar da zuwa yanzu tsanantar wannan cuta ta kyanda ta tilasta kulle makarantu.

    10 min
  • Karancin ruwa na haddasa tarin cutuka ga al'ummar arewacin Kamaru

    Shirin Lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda al’ummar yankin arewacin kamaru ke fuskanta matsalar rashin tsaftatacce kuma wadataccen ruwan sha ba, wanda ke haddasa gagarumar matsala ga lafiyar mazauna yankunan, wannan shi ne maudu’in da shirin na wannan mako zai mayar da hankali akai.

    Tsaftatacce kuma wadataccen ruwan sha na  matsayin ginshikin lafiyar jama’a wanda kuma rashin ke matsayin babbar barazanar bullar tarin cutuka na cikin wajen jikin bil’ada, sai dai samun ruwan sha ko na amfani ga galibin al’ummomin da ke rayuwa a yankin arewacin Kamaru na matukar wahala.

    A baya-bayan nan al’ummar yankin na ganin bullar cutuka da dama masu alaka da rashin tsaftataccen ruwan sha ko na amfani, yankin da kashi 43.5 na al’ummarsa ne kadai musamman mazauna karkara kan iya samun wadatacce kuma tsaftataccen ruwa.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shiri.

    11 min
  • Amfanin Azumi ga lafiyar jikin dan Adam

    Shirin Lafiya Jari ce a wannan karo ya mayar da hankali ne game da alfanun Azumi ga lafiyar jikin dan Adam. Masana kiwon lafiyar dai na bayyana cewar Azumi na taimakawa wajen rage kaifin wasu cutuka a jikin dan adam.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....

    10 min
  • Yadda ya kamata mai Azumi ya kula da kansa a lokacin zafi

    Shirin Lafiya Jari ce a wannan karo ya mayar da hankali ne kan irin cutukan da ke karuwa a lokutan Azumi musamman yadda a wannan karon ake gudanar da ibadar a cikin yanayi na tsananin zafi, wanda masana ke ganin akwai wasu naukan cutukan da ka iya bijorowa. Masana kiwon lafiya dai sun gargadi masu dauke da wasu nau'ukan cutuka kan irin matakan da ya kamata su dauka don kula da lafiyarsu.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....

    10 min

About Lafiya Jari ce

From the publisher's feed

Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi,…

More shows like Lafiya Jari ce

Labarai by RFI Hausa

Labarai

0 Listeners

Kasuwanci by RFI Hausa

Kasuwanci

0 Listeners

Muhallinka Rayuwarka by RFI Hausa

Muhallinka Rayuwarka

0 Listeners

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare by RFI Hausa

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

0 Listeners

Wasanni by RFI Hausa

Wasanni

0 Listeners

Dandalin Fasahar Fina-finai by RFI Hausa

Dandalin Fasahar Fina-finai

0 Listeners

Tarihin Afrika by RFI Hausa

Tarihin Afrika

0 Listeners

Al'adun Gargajiya by RFI Hausa

Al'adun Gargajiya

0 Listeners

Tambaya da Amsa by RFI Hausa

Tambaya da Amsa

0 Listeners

Ilimi Hasken Rayuwa by RFI Hausa

Ilimi Hasken Rayuwa

0 Listeners