Lafiya Jari ce

Lafiya Jari ce

By RFI Hausa
Download on the App Store

Lafiya Jari ce episodes

  • Yadda ƙungiyar ALIMA ta Faransa ke taimakawa wajen yaƙi da cutar yunwa a Najeriya

    Shirin lafiya jari ce a wannan makon ya mayar da hankali kan ta’azzarar cutar Tamowa ko kuma rashin sinadaran abinci mai gina jiki da ke addabar ƙananan yara a Najeriya, a wani yanayi da asusun UNICEF ke cewa duk yaro 1 cikin 3 na fama da matsalar ƙarancin abinci a ƙasar, wanda ke wakiltar kashi 37 cikin 100 na yawan yaran ƙasar ko kuma adadin yara miliyan 6.

    Duk da cewa tsawon lokaci wannan cuta ta ɗauka ta na addabar yara a Najeriyar, a wannan karon cutar ta tsananta a jihohin arewacin ƙasar wanda masana suka alaƙanta da matsaloli masu alaƙa da rashin tsaron da ya hana jama’a noma da kuma gushewar damunar bana da wuri, lamarin da ya ƙara yawan yaran da ke fama da cutar ta Tamowa ko kuma yunwa, dalilin da ya ja hankali ƙungiyoyin agaji da dama ciki har da ALIMA wato Alliance for International Medical Action ta Faransa wadda ke bayar da agajin lafiya a ƙasashe 13 ciki har da Najeriya.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....

    10 min
  • Irin kulawar da ya kamata iyaye su bai wa ƴaƴansu a yanayi na hunturu

    Shirin lafiya jari ce a wannan makon ya yi duba ne kan cutukan da ke barazana a lokacin sanyi, baya ga shawarwari kan yadda iyaye za su kula da lafiyar yaransu a irin wannan lokaci, musamman ganin cewa yaran ne sanyi ya fi yiwa illa fiye da manya.

    Dai dai lokacin da iskar hunturu ta fara kaɗawa a sassan jamhuriyar Nijar, jihar Difffa na sahun jihohin da wannan matsala ke tsananta matuka ta yadda a kowacce shekara ake ganin tarin waɗanda sanyi kan yiwa lafiyarsu illa.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.......

    11 min
  • Adadin masu kamuwa Cancer zai ninka sau 10 a Najeriya- Masana

    Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya mayar da hankali kan yadda cutar Cancer ko kuma Daji ko Najeriya ke ta'azzara a Najeriya a wani yanayi da ake da ƙarancin wayar da kai kan cutar duk kuwa da illar da ta ke ci gaba da yiwa jama'a.

    Hankulan masana a ɓangaren kiwon lafiya ya tashi ne matuƙa bayan hasashen da ke nuna yiwuwar alƙaluman masu kamuwa da cutar duk shekara a Najeriyar da yawansu ya kai dubu 70 ya iya ruɓanyawa fiye da ninki 10 nan da shekaru ƙalilan masu zuwa a ƙasar, a wani yanayi da har yanzu jama'a ke jahiltar cutar.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    10 min
  • Matsalar mace-macen mata masu juna biyu ta sake ta'azzara a Nijar

    Shirin Lafiya Jari ce a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan matsalar mace-macen mata masu juna biyu da jarirai walau a lokacin haihuwa ko kuma goyon ciki, matsalar da ke tsananin ta'azzara a Jamhuriyyar Nijar bayan da alƙaluma suka nuna yadda matsalar ke kwan-gaba-kwan-baya sakamakon dawowarta a baya-bayan nan bayan daƙileta a shekarun baya.

    Masana sun alaƙanta matsaloli masu alaƙa da rashin cin abinci mai gina jiki ko kuma rashin kulawar lafiya baya da rashin garkuwa mai ƙwari ga matan a jerin manyan dalilan da kan sabbaba mace-macen matan masu juna.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    11 min
  • Yadda ake samun ƙaruwar mace-macen kwab-ɗaya ko kuma mutuwar fuju’a

    Shirin Lafiya Jari ce a wannan makon ya nazarci yawaitar mace-macen kwab-ɗaya ko kuma mutuwar fuju’a da ake ganin ta’azzararsu a wannan lokaci musamman a sassan Najeriya a wani yanayi da matsi ko kuma tsadar rayuwa ke ci gaba da galabaitar da jama’a.

    Dai dai lokacin da masana ke alaƙanta wannan matsala ta mutuwar far ɗaya da wasu kwantattun cutuka da yanayi kan tayar da su a lokaci guda, wani bincike baya-bayan nan ya danganta tsananin damuwa da yawaitar tunane-tunne halin rayuwa a matsayin ummul aba’isin kamuwa da wasu cutuka da ke kisan jama’a. 

    Tuni dai masana a ɓangaren kiwon lafiya suka tsananta kiraye-kirayen ganin jama’a sun mayar da hankalin wajen sanin halin da lafiyarsu ke ciki don kaucewa mutuwar ta kwaf ɗaya.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.......

    11 min
  • Lafiya Jari ce: Illar da hayaƙin girki ke yiwa lafiyar idon Mata

    A wannan makon shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan wani gargaɗin masana game da illar hayaƙi ga lafiyar jama’a a wani yanayi da masanan ke ganin mazauna garuruwa irin Kano da Sokoto da Kwara baya ga kaso mai yawa na jihohin arewacin Najeriya na cikin haɗarin kamuwa da cutukan masu alaƙa da numfashi sakamakon yadda suka dogara da itace ko kuma gawayi wajen yin girki.

    A ɓangare guda wasu ƙwararrun na ganin matan da suka shafe lokaci suna girki da itace ka iya fuskantar matsalar ido, tambayar a nan ita ce ko matan na da masaniya kan illar hayakin girki ga lafiyar idonsu? Ku biyo mu a cikin shirin don sauraren mahangar masana da kuma yadda Mata ke kallon illar ta hayaƙin girki ga lafiyarsu.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin....

    11 min
  • Ƙuncin rayuwa na jefa ɗimbin ƴan Najeriya cikin tsananin damuwa - Rahoto

    Shirin Lafiya Jari ce a wannan makon ya mayar da hankali kan matsalar damuwa mai dankwafarwa ko tsananin damuwa da ake kira Depression, cutar da ake ganin ta’azzararta a baya-bayan nan tsakanin ƙasashe masu tasowa musamman waɗanda ke fama da matsi ko kuma ƙuncin rayuwa.

    Wasu bayanan ƙwararru yayin bikin ranar lafiyar ƙwaƙwalwa da ya gudana a farkon watan nan, ya nuna yadda matsi da ƙunchin rayuwa ya jefa miliyoyin ƴan Najeriya a tsananin damuwar ko kuma damuwa mai dankwafarwa, matsalar da likitoci suka yi gargaɗin cewa ka iya kaiwa ga taɓin ƙwaƙwalwa.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu........

    10 min
  • Yadda mutane ke kauracewa yin gwaje-gwajen lafiya na wajibi

    Shirin Lafiya Jari ce a wannan makon yayi duba ne kan ƙalubalen da fannin lafiya ke fuskanta na yadda ake gani a halin yanzu jama’a ke tsoro ko kuma kaucewa gwaje-gwajen lafiya ciki kuwa da har da wajibi da suka ƙunshi hawajini da nau’in jini ko kuma rukuninsa duk kuwa da muhimmancin hakan ga lafiyarsu.

    A baya-bayan nan bincike ya gano yadda jama’a kan kaucewa yin gwaje-gwaje kama daga na wajibi ko kuma a lokacin kamuwa da cutuka, walau ko saboda tsoron gano wasu nau’in cutuka da ke tare da su ko kuma wani dalili na daban.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu......

    10 min

About Lafiya Jari ce

From the publisher's feed

Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi,…

More shows like Lafiya Jari ce

Labarai by RFI Hausa

Labarai

0 Listeners

Kasuwanci by RFI Hausa

Kasuwanci

0 Listeners

Muhallinka Rayuwarka by RFI Hausa

Muhallinka Rayuwarka

0 Listeners

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare by RFI Hausa

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

0 Listeners

Wasanni by RFI Hausa

Wasanni

0 Listeners

Dandalin Fasahar Fina-finai by RFI Hausa

Dandalin Fasahar Fina-finai

0 Listeners

Tarihin Afrika by RFI Hausa

Tarihin Afrika

0 Listeners

Al'adun Gargajiya by RFI Hausa

Al'adun Gargajiya

0 Listeners

Tambaya da Amsa by RFI Hausa

Tambaya da Amsa

0 Listeners

Ilimi Hasken Rayuwa by RFI Hausa

Ilimi Hasken Rayuwa

0 Listeners