
Sign up to save your podcasts
Or


Shirin Lafiya Jari ce a wannan karo ya mayar da hankali ne kan yadda aka gudanar da gangamin rigakafin cutar shan inna wato Polio a Jamhuriyar Kamaru don dakile bazuwarta. A baya-bayan nan ne dai ake ganin bullatar cutar a wasu sassan kasar, lamarin da ya sanya mahukunta tashi tsaye don yin rigakafin cutar.
Sama da yara dubu dari 9 da 48 ne aka yi wa rigakafin a fadin jahohi 10 na Kamaru, a aikin da aka kwashe tsawon kwanaki uku ana yi.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....
A wannan mako shirin ya mayar da hankali kan nau’ikan cutakan da ba a fiya mayar da hankali wajen yakarsu ba musamman a kasashe masu tasowa irin Najeriya, wannan nau’in cutuka kuwa sun kunshi kansar mafitsara ko kuma Prostate Cancer, nau’in kansar da ke matsayin mafi hadari ga maza, amma kuma ba ta samun kula duk da yadda ta ke kisan akalla mutum dubu 8 duk shekara a Najeriya.
Shirin Lafiya Jari ce a wannan karo ya mayar da hankali ne kan cutar cizon mahaukacin kare ko kuma Rabies a turance, bayan da bincike ya nuna cewar cutar na karuwa a Najeriya duk da cewa babu cikakkun alkaluman wadanda cutar ta shafa saboda karancin kawo rahoton cutar ga mahukunta.
Sai dai wasu alkaluman hukumar dakile yaduwar cutuka ta Najeriyar NDDC sun nuna cewa daga shekarar 2017 zuwa 2022 akwai akalla mutane 998 da kuma karnuka 273 da suka harbu da cutar ta Rabies ko kuma cizon mahaukacin kare.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.....
A wannan makon shirin Lafiya Jari ce ya mayar da hankali ne kan cutar kazuwa ko kuma Smallpox a turance, cutar da ke sahun cutuka masu matukar hadari da ke haddasa kuraje masu matukar kaikayi da mashasshara da kuma hana barci, wadda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta sanar da kawar da ita daga ban kasa tun a shekarar 1980 amma kuma duk da haka ake ganin bullarta lokaci zuwa lokaci.
Cutar ta kazuwa wadda ake alakantawa da kazanta a baya-bayan nan ne aka samu barkewarta a wasu kauyukan Jihar Maradi ta Jamhuriyyar Nijar, inda masana ke cewa zuwa yanzu akwai fiye da mutum dubu 3 da suka harbu, kuma kaso mai yawa na Almajirai da magidanta sai kuma kananan yara musamman a kauyukan Surori zuwa Tsibiri da kuma garin Udal, wanda ke matsayin karon farko da aka ga bullar cutar bayan shafe tsawon shekaru ba tare da jin duriyarta ba.
Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Azima Bashir Aminu....
A wannan makon shirin ya mayar da hankali kan yawaitar gurbatattun jami’an lafiya a asibitocin Najeriya wanda ke da nasaba da kodai rashin samun cikakken horo a kwalejojin lafiya ko kuma samun horon irin wadannan makarantu amma na bogi.
A baya-bayan nan ana yawan ganin yadda ake bude tarin makarantu masu zaman kansu a sassan Najeriya da sunan horar da jami’an lafiya kama daga kwalejoji har da jami’o’I wadanda wasu daga cikinsu kan rasa sahalewar mahukuntan saboda rashin cancanta.
Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya yi duba ne kan illar dafin miciji ga lafiyar bil'adama dai dai lokacin da asibiti daya tilo da ke lura da wadanda suka gamu da cizon na maciji ke ganin koma baya.
Asibitin wanda ke jihar Gombe a Najeriya yanzu haka na fuskantar kalubale rashin tafiyarwa ta yadda baya iya bayar da gudunmawa kamar yadda ya dace ga dimbin majinyatan da ke ziyartarshi bayan haduwa da cizon maciji.
Baya ga rashin wuta da rashin isassun jami'an kula da marasa lafiya, matsalar tsadar magunguna a asibitin na matsayin dalilin da ke hana mutane zuwa duba lafiyarsu ko da sun hadu da ibtila'in na cizon maciji.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...........
A wannan mako shirin ya mayar da hankali ne kan ci gaban da aka samu na fara amfani da fasahar fida ba tare da tsaga jikin majinyaci ba a Najeriya, a wani yunkuri na rage dogaro da kasashen ketare wajen irin wannan fida.
Wannan ci gaba dai ya biyo bayan koken kungiyar likitocin sashen gwaje-gwajen cutuka ta Najeriya wadda a yayin taronta na 206 ta bayyana cewa lokaci yayi da ya kamata a ce Najeriya ta zama kasar da za a rika tururuwa don shigowa neman magani idan har da gwamnatoci sun yi abin da ya dace. kuma dangane da haka ne asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke garin Bauchi, ya kaddamar da wata na’urar fede marar lafiya ba tare da tsaga jikinsa ba, kamar yadda shugaban asibitin Dr Yusuf Jibril Bara ke cewa.
Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wanna makon tare da Murtala Adamu Ibarhim ya maida hankali ne kan shirin gwamnatin Najeriya na sake daukar likitoci da sauran jami'an kiwon lafiya wadanda suka yi ritaya daga aiki, a wani kokari na cike gibin karancin jami'an kiwon lafiya a kasar, masamman guraben wadanda suka tsere zuwa kasashen waje domin samun albashi mai soka.
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon ya tattauna ne kan musabbabin kamuwa da ciwon koda a daidai lokacin da wasu alkaluma ke nuni da cewa, akwai mutane kimanin miliyan 17 da ke fama da cutar a Najeriya.
Shirin ya kuma yi dubi kan kalubalen da masu fama da cutar ke fuskanta musamman dangane da samun kudin kwanke kodar a Najeriya ko kuma kudin sayen maganin cutar.
Shirin ya tattaunawa da kwararrun likitoci wadanda suka yi cikakken bayani kan yadda wannan cuta ke kama jama'a da kuma yadda za a kauce mata.
Kazalika shirin ya zanta da masu fama da cutar ta koda, inda suka yi bayani kan yadda suke ji a jikinsu da kuma hanyar da suke bi wajen kokarin magance ta.
Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon ya tattauna ne kan musabbabin kamuwa da ciwon koda a daidai lokacin da wasu alkaluma ke nuni da cewa, akwai matasa kimanin miliyan 5 da ke fama da ciwon koda a kasar Ghana.
Shirin ya tattaunawa da kwararrun likitoci wadanda suka yi cikakken bayani kan yadda wannan cuta ke kama jama'a da kuma yadda za a kauce mata.
Kazalika shirin ya zanta da masu fama da cutar taa koda, inda suka yi bayani kan yadda suke ji a jikinsu da kuma hanyar da suke bi wajen kokarin magance ta.
Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu
From the publisher's feed
Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi,…

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners