Lafiya Jari ce

Lafiya Jari ce

By RFI Hausa
Download on the App Store

Lafiya Jari ce episodes

  • Yadda shirin tallafi ga masu cutar ƙoda zai amfanar da ɗimbin jama'ar Najeriya

    Shirin Lafiya Jari ce a wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan matakin gwamnatin Najeriya na rage farashin wankin ƙoda ko kuma Dialysis, daga Naira dubu Hamsin ko fiye da haka zuwa Naira dubu 12 kacal.

    Tuni wannan mataki ya Faranta ran ɗimbin ƴan Najeriya musamman waɗanda ke da ƴan uwan masu fama da wannan lalura da ke da matuƙar cin kuɗi, kodayake murna ta fara komawa jiki, bayan cikakken bayani kan wannan tagomashi ya nuna cewa babu kaso mai yawa na jihohin Arewa maso yammacin Najeriya, duk kuwa da yadda suke da ɗimbin masu fama da wannan lalura.

    Ku latsa alamar sauti don sauraren shirin....

    10 min
  • Muhimmancin shayar da jarirai nonon uwa zallah a watannin shidan farko

     

    A wannan makon shirin ya yi duba kan tsarin nan na shayar da nonon uwa zalla ga jarirai tun daga haihuwa har zuwa watanni 6 ba tare da silki ba, tsarin da ake cigaba da ganin mabanbantan ra’ayoyi hatta daga iyaye dama wasu jami’an lafiya.

    Bisa al’ada kowanne makon farko na watan Agusta na matsayin makon shayar da Nonon uwa zalla da ake kira Exclusive Breast Feeding a turance, da nufin ƙarfafa gwiwar iyaye wajen rungumar tsarin na shayar da Nonon Uwa zalla ga jarirai, makon da a wannan shekarar ke da taken Fifita tsarin shayar da jarirai Nono zalla don samar tallafi mai ɗorewa.

    11 min
  • Matakin Amurka ka iya haifar da koma baya ga shirin yaki da cutar HIV a Najeriya

    Shirin ya mayar da hankali ne kan yadda matakin Amurka na janye tallafin da take ba wa ɓangaren kula da masu fama da cuta mai karya garkuwa jiki ta HIV da ake fargabar zai iya haifar da koma baya ga shirin yaƙi da cutar.

    Tuni hukumomi a duniya suka fara tofa albarkacin bakinsu kan wannan mataki da shugaban Amurka, Donald Trump ya ɗauka, wanda ake ganin zai fi yin tasiri ne ga nahiyar Afirka.

    Tuni mujallar Lancet ta Biritaniya ta yi hasashen cewa matakin na Donald Trump na iya haifar da mutuwar mutane sama da miliyan 14 nan da shekarar 2030, ciki har da yara sama da miliyan 4.5 'yan kasa da shekaru biyar.

    Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashi Aminu.

    11 min
  • Yadda matsalolin tsaro ke haddasa ƙarancin abinci da ke assasa cutukan yunwa

    Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya yi duba kan yadda matsalolin tsaro ke haddasa ƙarancin abinci wanda ke matsayin masabbabin cutuka masu alaƙa da yunwa musamman a yankunan jihohin Sokoto da Zamfara da matsalolin ƴanbindiga suka zama ruwan dare.

    Shirin ya tattauna da masana daga yankunan waɗanda suka bayar da shawarwari kan yadda za a tunƙari matsalolin na ƙarancin abinci dama cutukan da suke haddasawa.

    Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.

    10 min
  • Yadda Najeriya ta tashi tsaye wajen yaƙi da cutar kansar bakin mahaifa

    Shirin Lafiya jari ce a wannan makon ya mayar da hankali ne kan wasu alƙaluman baya-bayan nan da ke nuna yadda mata dubu 14 ke kamuwa da cutar kansar bakin mahaifa ko kuma cervical cancer duk shekara a Najeriya, alƙaluman da ke da matuƙar tayar da hankali, ganin yadda wannan cuta ke kisa ba ƙaƙƙautawa ga duk waɗanda suka kamu da ita.

    Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.........

    10 min
  • Irin rawar da Ungozomar gargajiya ke takawa wajen taimakawa mata masu juna biyu

    Shirin Lafiya Jari ce na wannan mako zai mayar da hankali kan yadda ƙarancin asibitoci ko malaman jinya a yankunan karkara, da kuma rashin kyawun hanyoyin zuwa asibiti musamman ga mata masu juna biyu na tilasta wa matan haihuwar gida saɓanin asibiti, ta yadda galibi Ungozomar gargajiya ke matsayin masu ceto a irin wannan yanayi.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu..........

    11 min

About Lafiya Jari ce

From the publisher's feed

Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi,…

More shows like Lafiya Jari ce

Labarai by RFI Hausa

Labarai

0 Listeners

Kasuwanci by RFI Hausa

Kasuwanci

0 Listeners

Muhallinka Rayuwarka by RFI Hausa

Muhallinka Rayuwarka

0 Listeners

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare by RFI Hausa

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

0 Listeners

Wasanni by RFI Hausa

Wasanni

0 Listeners

Dandalin Fasahar Fina-finai by RFI Hausa

Dandalin Fasahar Fina-finai

0 Listeners

Tarihin Afrika by RFI Hausa

Tarihin Afrika

0 Listeners

Al'adun Gargajiya by RFI Hausa

Al'adun Gargajiya

0 Listeners

Tambaya da Amsa by RFI Hausa

Tambaya da Amsa

0 Listeners

Ilimi Hasken Rayuwa by RFI Hausa

Ilimi Hasken Rayuwa

0 Listeners