Shirin Muhallinka Rayuwarka ya tattauna ne game da rikicin Makiyaya da Manoma a Najeriya da kuma nazarin da gwamnatin Tarayya ke yi na farfadowa tare sa samar da sabbin hurumin kiyo ga makiyaya domin magance rikicin. Shirin ya tattauna da Kungiyoyin Makiyaya da Manoma tare da ji daga bakin masana akan yadda ya dace a tsara hurumin na Kiyo.