Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

By RFI Hausa
Download on the App Store

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare episodes

  • Ra'ayoyin masu sauraro kan jingine shirin ƙara kuɗin mai a Nijar

    Mahukuntan Jamhuriyar Nijar sun jingine batun ƙara farashin mai duk da cewa Majalisar Dokokin Riƙon Kwaryar ƙasar ta bayar da shawarar yin wannan ƙari don magance ƙaracin makamashi da ake fama da shi a ƙasar.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ta sanar da wani shirin rage farashin mai a tsawon wata ɗaya domin sauwaƙa wa jama’a.

    Latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyin jama'a...

    10 min
  • Ra'ayoyin masu saurare kan fatan ci gaba da haƙo man fetur a wasu sassan arewacin Najeriya

    Taron gwamnonin jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya da ya gudana a ƙarshen mako, ya buƙaci gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta gaggauta farfaɗo da aikin binciken man fetur da aka faro tsawon shekaru a yankin.

    Kazalika taron ya buƙaci gwamnatin da ta mayar da hankali wajen gyara layin dogon da ya haɗa biranen Port-court-Jos-Bauchi-Gombe zuwa Maiduguri saboda muhimmancinsa  wajen buƙasa tattalin arzikin al’ummar yankin.

    Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

    11 min
  • Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa mabanbanta

    Yau juma'a kamar yadda aka saba, sashen Hausa na RFI na bai wa masu sauraro damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwan dake ci musu tuwo a ƙwarya, kama daga siyasa, tattalin arziƙi, tsaro, zamantakewa da dai sauransu.

    Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

    11 min
  • Ra'ayoyin masu sauraro kan ƴan aikin jarida dake fuskantar tarnaƙi a Afrika

    Ƴancin aikin jarida na ci gaba da fuskantar tarnaƙi a wasu ƙasashen Afirka, saboda yayin da wasu ke fuskantar tursasawa a Najeriya, a Jamhuriyar Nijar kuwa ana tsare da Moussa Tchangari kusan shekaru biyu ba tare da shara’a ba, yayin da a hannu ɗaya, wani ɗanjaridar wato Moussa Kaka ya ɓata yau kwanaki 16 kenan.

    A can kuwa Mali ko shekaran jiya litinin ma an yanke wa wani ɗanjaridar hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari, kamar dai yadda ake cafkewa tare da tilasta ƴanjaridar da ra’ayoyinsu suka bambanta da na gwamnati, shiga aikin soji a Burkina Faso.

    Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai yau.

    Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

    11 min
  • Ra'ayoyin masu sauraro kan hauhawar farashin man fetur a Najeriya

    Hauhawar farashin man fetur na ci gaba da haifar da tarin matsaloli ga al’ummar Najeriya, inda a jihohi irinsu Sokoto, Kebbi da Zamfara, farashin lita ya doshi Naira dubu ɗaya da 500 a halin yanzu kuma kusan hakan farashin yake a mafi yawan jihohin arewacimn ƙasar.

    Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai yau, musamman game da yadda ake samun hauhawar farashin akai-akai da kuma yadda wataƙila hakan ke shafar kasuwanci da kuma sufuri a yankunanku.

    Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

    10 min
  • Ranar yaƙi da jahilci ta duniya a bana ya duba yadda za a inganta ilimin manya

    Ranar takwas ga watan Satumban kowacce shekara, rana ce da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware, tun a shekarar  1960 a matsayin ranar yaƙi da jahilci, inda ake mayar da hankali wajen faɗakar da jama'ar a sassan duniya mahimmancin ilimi da samar da tsari ko dabarun koyar da mutanen da basu samu dama ba.

    A mafi yawan ƙasashe dai an sha aiwatar da tsarin yaƙi da jahilci da ke bai wa dattijai ko masu manyan shekaru damar iya koyon rubutu da karatu a rayuwarsu.

    Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

    11 min
  • Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa mabanbanta

    Kamar yadda aka saba ko wace rana irin ta yau Juma’a, muna baku damar tofa albarkacin bakin ku kan wasu abubuwa da ke ci muku tuwo a ƙwarya kama daga siyasa da tattalin arziƙi da zamantakewa da dai sauransu.

    To yau ba ta sauya zani ba, sai ku latsa alamar sauti don sauraren shirin...

    12 min
  • Ra'ayoyin masu sauraro kan kalaman tinzira jama'a da wasu ƴan siyasa suke

    A Najeriya ana ci gaba da mayar da martani mai zafi sakamakon kalaman da shugaban ƙaramar hukumar Kuje da ke birnin Abuja Mista Samuel Shekwolo ya furta, kan cewa duk wanda baya goyon bayan jam’iyya mai mulki ta APC ya fice daga karamar hukumar.

    Yayin da ake tunkarar zabe a Najeriya, sannu a hankali kalaman tunzuri da yiwa jama’a barazana a karuwa a tsakanin yan siyasa musamman daga bangaren jam’iyya mai mulki, ganin yadda a baya-bayan nan wani sanata daga jihar Osun ya umarci magoya bayan jam’iyyar da su kashe abokan hammaya a duk inda suka hadu.

    Shin yaya kuke kallon hadarin irin waɗannan kalamai yayinda ake shirye-shiryen zabe a kasar?

    Kuna ganin Najeriya zata iya daukar mataki kan masu aikata wannan katobara ganin yadda har yanzu ba’a kai ga hukunta wancan sanata ba?

    Sai ku bayyana mana ra’ayoyinku kamar yadda aka saba.

    11 min

About Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

From the publisher's feed

Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Al’umma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa…

More shows like Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Dandalin Fasahar Fina-finai by RFI Hausa

Dandalin Fasahar Fina-finai

0 Listeners

Ilimi Hasken Rayuwa by RFI Hausa

Ilimi Hasken Rayuwa

0 Listeners

Kida, Al'adu da Fina-Finai by RFI Hausa

Kida, Al'adu da Fina-Finai

1 Listeners

Lafiya Jari ce by RFI Hausa

Lafiya Jari ce

0 Listeners

Wasanni by RFI Hausa

Wasanni

0 Listeners

Mu Zagaya Duniya by RFI Hausa

Mu Zagaya Duniya

0 Listeners

Muhallinka Rayuwarka by RFI Hausa

Muhallinka Rayuwarka

0 Listeners

Tambaya da Amsa by RFI Hausa

Tambaya da Amsa

0 Listeners

Tarihin Afrika by RFI Hausa

Tarihin Afrika

0 Listeners