Ilimi Hasken Rayuwa

Ilimi Hasken Rayuwa

By RFI HausaEducation
Download on the App Store

Ilimi Hasken Rayuwa episodes

  • Najeriya: saɓanin alƙaluma kan jihar da ɗalibanta ke kan gaba a cin jarabawar NECO

    A yau shirin zai leƙa Najeriya, inda aka samu saɓani ta fuskar alƙaluma a fannin ilimi, bayan fitar da sakamakon jarabawar ƙasa ta NECO na shekarar 2026, gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa jihar ce ta zo ta ɗaya a fadin ƙasar.

    Sai dai, wani bincike mai zurfi da jaridar Premium Times ta yi, ya musanta wannan iƙirari, inda ta ajiye jihar a matsayi na 31.

    Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

    11 min
  • Jigawa ta gabatar da tsarin rage barace-baracen Almajirai a jihar

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan daɗaɗɗen batun nan na yaran da basa zuwa makaranta a Najeriya matsalar da har kawo yanzu ta ƙi ci taki cinyewa.

    Wani Rahoton UNICEF ya bayyana jihohin Kano da Jigawa da kuma Katsina a matsayin jihohin da ke da rinjayen yaren da basa zuwa Makaranta, inda a jumlace ƙasar ta yammacin Afrika ke da yara fiye da miliyan 18 da basa zuwa Makaranta, galibinsu a arewacin ƙasar.

    Tuni Jihar Jigawa ta ɗaura ɗamarar yaƙi da wannan matsala, inda ta gabatar da wani sabon tsarin mayar da ɗimbin yara makarantu.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    10 min
  • Yadda matasa suka ƙera jirgi maras matuƙi mai cin Kilomita 30 a Kano

    Shirin a wannan makon ya leka Kanon Najeriya, inda aka gano wani sabon tarihin bunkasar kimiyya da fasaha da matasan yankin ke jagoranta.

    Wannan gagarumar bajinta dai wani matashi Abubakar Waiya, wanda ya daɗe yana fafutukar kera na'urorin shawagi ne ya ƙera jirgi maras matuƙi domin taimakawa ɓangaren tsaro da kuma boma.

    Jirgin da ya kera a yanzu yana da ikon tashi da kansa har na tsawon kilomita 30 ba tare da ya ɓace ba.

    Wannan na'ura tana da aiyuka na musamman da aka tsara ta don yi, kamar feshin maganin ƙwari a gonaki na zamani da kuma kai magungunan gaggawa zuwa yankunan karkara da motoci ba su iya zuwa saboda rashin hanya.

    Duk da wannan gagarumar nasara, babban ƙalubalen da ke gaban matasan shi ne tsarin dokoki na ƙasa.

    Masu fafutuka na ganin cewa, idan har gwamnati da masu ruwa da tsaki suka ba wa waɗannan matasa dama da goyon baya, wannan ƙoƙari daga birnin Kano zai zama tushen samar da dabarun tsaro da aikin gona na zamani ga ɗaukacin yammacin Afirka.

    Tambayar da ta rage anan ita ce: Shin gwamnati za ta tallafa wa wannan fasaha ta gida don ta bunkasa, ko kuwa za a zura ido ta ɓace ne?

    11 min
  • Makomar ilimin yara a Kano na cikin halin rashin tabbas

    Shirin na wannan makon cigaba ne kan wanda muka gabatar a makon jiya, wanda ya gano yadda yara a wasu yankunan jihar Kano basa zuwa makaranta saboda yawon tallace-tallace domin tara kudin kayan ɗaki. Yayin da su kuma mazan suke diban yashi da fasa Dutse, da sunan wai su taso suna da sana'ar dogaro da kai.

    Yankunan da wannan lamari yafi kamari sun hada da Challawa, Kafin Maiyaki, Madobi, Gora, da Kanwa. Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata mun kawo rahoton yadda wasu makarantu suka koma dandalin shaye-shaye a garin Meshumi dake karamar hukumar Ungogo.

    10 min
  • Yadda makomar ilimin yaran karkara a Najeriya ke cikin rashin tabbas

    A wannan makon, shirin ya nufi yankunan karkara, inda inda gine-ginen makarantu ke ci gaba da kasancewa a matsayin kango, kasancewar babu dalibai.

    A wasu wuraren kuma, azuzuwan sun zama fanko, yayin da matasa da yara suka ƙaurace wa shiga, ‘yan mata na fita birni yin tallace-tallace, su kuma samari na dambatawa da aikin ƙwadagon fasa duwatsu da ɗiban yashi.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da sabon rahoton hukumar UNICEF ya nuna cewa, jihohin Kano, Katsina, da Jigawa ne ke kan gaba a faɗin Najeriya wajen yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, inda a faɗin kasar kuwa, akwai yara sama da miliyan goma sha takwas da dubu ɗari uku da makoma ta iliminsu ke cikin haɗari.

    Sau da yawa, wannan zargi na komawa ga gwamnati, sai dai abin tambayar shine, shin ko laifin na iyaye ne da al'umma, ko kuwa suma hukumomi akwai nasu kason?

    Mun ziyarci garin Meshumi da ke karamar hukumar Ungoggo a jihar Kano, inda shirin ya tarar makarantar firamare na nan a gine, amma dakin karatu ya zama kufai.

    Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin, tare da Shamsiyya Haruna

    10 min
  • Taron ƙaddamar da littafin tarihi na wani fitaccen matashi a Kanon Najeriya

    Shirin na wannan mako ya mayar da hankali ne kan taron ƙaddamar da sabon littafin tarihin nan mai suna 'Mu San Magabata', wanda fitaccen matashin marubuci Kabiru Ahmad Kwalli ya rubuta da aka gudanar a jihar Kanon Najeriya.

    Taron ya haɗa masana, sarakuna, da ɗandazon al'umma domin duba yadda za a ceto tarihin ƙasar Hausa da ke shirin bacewa.

    Wannan littafi, kamar yadda masana da dama suka bayyana, ya zo ne a daidai lokacin da matasan yanzu ke ƙara nisanta da asalin tarihinsu.

    To ko me ya sa mawallafin, Kabiru Ahmad Kwalli,  ya ɗauki tsawon lokaci yana wannan bincike? Ga abinda ya shaida mana lokacin da muke zantawa da shi.

    11 min
  • Yadda aka gudanar da taron manyan masana na duniya a birnin Lagos

    A wannan makon, shirin ya mayar da hankali ne kan babban taron ƙungiyar Lagos Studies Association karo na goma da aka kammala a ƙarshen mako, wanda ya saba haɗa masana, malaman jami'o'i, da masu bincike daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙasashen waje domin tattauna halin da ilimi yake ciki a nahiyar Afirka cikin wannan ƙarni.

    Wannan taro, wanda aka kafa shi shekaru goma da suka gabata a birnin New York, an dawo da shi gida Afirka domin tattauna ainihin matsaloli da ci gaban nahiyar ke fuskanta, kuma a bana, fiye da rukunonin tattaunawa 340 ne aka shirya, inda aka haɗa masana daga sassan duniya.

    Shekarar 2026 ta yi daidai da cikar kungiyar LSA shekaru 10 da kafuwa, inda aka gudanar da taron ƙarƙashin taken makomar ilimin nahiyar Afirka a wannan ƙarni.

    Wani sashe mai muhimmanci a taron shi ne tattaunawa kan littafi na musamman mai suna 'Our Digital Lives and Indigenous Pathways', wanda masana suka duba yadda za a haɗa fasahar zamani da dabarun gargajiya na Afirka don samun ci gaba mai dorewa.

    Baya ga tattaunawar kimiyya, taron ya haɗa da baje kolin fasaha na musamman mai taken 'Histories on Scissors: The Black Essence on the Map of Being' wanda Dominic James Aboi daga Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria ya gabatar. An kuma tattauna makaloli kan addini da rashin addini a Arewacin Najeriya.

    An dai gudanar da wannan taro ne domin nazarin al'adun zamani da na gargajiya, inda masana suka gabatar da maƙaloli kan tarihin Afirka, al'adu, da kafafen yaɗa labarai haɗi da baje kolin dabarun bincike na zamani.

    A taron na bana, masana sun gano muhimman abubuwa da suka shafi makomar nahiyar Afirka ta fuskar ilimi, zamantakewa, da fasaha, kuma babban jigon da aka mayar da hankali akai shi ne yadda za a fassara binciken ilimi ya zama abin da zai amfani rayuwar al'umma kai-tsaye.

    Haka zalika an gano cewa ko da yake yawan binciken da masana da ke zaune a cikin Afirka ke fitarwa ya ƙaru sosai, amma ingancinsa da kuma bayyanarsa a manyan jaridun ilimi na duniya ya ragu sosai.

    10 min

About Ilimi Hasken Rayuwa

From the publisher's feed

Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken…

More shows like Ilimi Hasken Rayuwa

Dandalin Fasahar Fina-finai by RFI Hausa

Dandalin Fasahar Fina-finai

0 Listeners

Kida, Al'adu da Fina-Finai by RFI Hausa

Kida, Al'adu da Fina-Finai

1 Listeners

Lafiya Jari ce by RFI Hausa

Lafiya Jari ce

0 Listeners

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare by RFI Hausa

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

0 Listeners

Wasanni by RFI Hausa

Wasanni

0 Listeners

Mu Zagaya Duniya by RFI Hausa

Mu Zagaya Duniya

0 Listeners

Muhallinka Rayuwarka by RFI Hausa

Muhallinka Rayuwarka

0 Listeners

Tambaya da Amsa by RFI Hausa

Tambaya da Amsa

0 Listeners

Tarihin Afrika by RFI Hausa

Tarihin Afrika

0 Listeners