Mu Zagaya Duniya

Mu Zagaya Duniya

By RFI Hausa
Download on the App Store

Mu Zagaya Duniya episodes

  • "Mu zagaya Duniya" bitar muhimman labaran da suka faru a makon da ya gabata

    Kamar kowanne mako shirin "Mu zagaya Duniya" ya yi bitar muhimman labaran da suka faru a mako da muke bankwana da shi daga sassa daban-daban na duniya, ciki kuwa har da rikicin gabas ta tsakiya musamman yadda aka cika shekaru 3 cif da faro yaƙin Isra’ila a Gaza daya kashe fararen hula fiye da dubu 70 wanda kuma shi ya assasa sauran rikice-rikicen da ake gani a yankin, kana a Najeriya da Nijar muka duba halin da ake ciki game da tsadar man fetur sai kuma matsalar tsaro.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....

    22 min
  • Shugaban Faransa ya bayyana halin da ake ciki a zirin Gaza a matsayin abin kunya ga duniya

    A yau shirin ya yi waiwaye kan bankado yadda wasu fitattun yan siyasa a Najeriya suka wawure makudan kudade tare da mallakar kadarori a Amurka, sai Hukumar Lafiya ta Duniya WHO da ta fara gwajin allurar Ervebo don daƙile cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo, da kuma fassarar kalaman shugaban Faransa Emmanuel Macron a babban taron MDD da ya bayyana halin da ake ciki a zirin Gaza na Palasdinu a matsayin babban abin kunya ga ƙasashen duniya.

    Masu bincike da suka ɓanƙado yadda jami’an gwamnatin Najeriya na baya da na yanzu suka wawure makuɗan kuɗaɗen talakawa wajen sayen manyan gidaje na ƙasaita a Amurka, sun ce yaƙi da ta’addanci na daga cikin manyan hanyoyi da ake amfani da shi wajen satar dukiyar jama’a a Najeriya.

    Haka zalika, kotun sasanta rikicin kasuwancin ta duniya dake birnin Paris na Faransa, ta yi watsi da buƙatar Kamfanin Sunrise da ya nemi Najeriya ta biya shi diyyar kuɗi dala miliyan 400.

    21 min
  • Ana ci gaba da tsokaci kan mutuwar mutane a hannun Civil Defence na jihar Neja

    Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan makon ya tabo batun mutuwar matasa sama da 30 a jihar Neja da ke Najeriya a hannun hukumar tsaro ta Civil Defence. Haka nan Gwamantin Guinea ta aike da gargaɗi a hukumance ga kafofin yaɗa labaran Faransa game da yadda suke kiran sunan shugaban ƙasar, sai kuma Majalisar Ɗinkin Duniya da ta buƙaci masu bincike na ƙasa da ƙasa su karaɗe ilahirin Zirin Gaza, domin tattara hujjoji kan ɗaruruwan gawarwakin mutanen da ake zaƙuluwa daga ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine.

    Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna............

    21 min
  • Dangote ya buɗewa al'uma ƙofar shiga a dama dasu a harkokin matatar mai

    Shirin mu zagaya Duniya na wannan ya ba da hankali ne akan yadda Attajirin Afirka Aliko Dangote ya buɗe ƙofar sayar da hannayen jari ga jama'ar Najeriya, sai kuma matakin da mahukuntan Nijar suka ɗauka na umartar masu ababen hawa dasu je Yamai babban birnin ƙasar domin duba lafiyar ababen hawansu, sai batun ladan da Shigaban Amurka Donald Trump ya sanya ladan Dala dubu biyar-biyar ga Amurkawa idan har jam'iyarsa ta Republican ta samu nasara a zaɓen tsakiyar wa'adi.  

    21 min
  • Yunkurin juyin mulki a Nijar ya ci gaba da ɗaukar hankali a faɗin duniya.

    A wannan makon shirin Mu Zagaya Duniya ya yi waiwayen kan sukar kalaman shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da ya yi na cewa arewacin kasar ya fi amfana da manufofinsa, sai batun juyin yunkurin juyin mulkin Nijar da ya dauki hankali, sai rahoton MDD da ya gano katsalandan din kasashen waje ne ke rura wutar rikicin Sudan, sai luguden wutar da aka yi musaya tsakanin Amurka da Iran da ya janyo asarar rayuka.

    A Najeriya, jam’iyyun adawa sun fara tsara yadda za su kayar da gwamnatin APC mai mulkin ƙasar ta wajen haɗakar da za ta fitar da ɗan takara ɗaya mai ƙarfi da zai iya gwabzawa da shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027, inda

    ƙungiyar  G-100, wadda ta tsara wannan haɗaka ta kawo shawarar cewa duk wanda ya samu takarar, zai yi wa’adi guda na shekaru 4  ne kacal.

    Haka zalika, ikirarin da shugaba Bola Tinubu ya yi cewa yankin arewacin ƙasar ce ta fi cin gajiyar manufofinsa na  sauye-sauyen tattalin arziƙi ya janyo suka daga  masu ruwa da tsaki, inda ƙungiyar al’ummar Arewacin ƙasar da wasu ƙungiyoyin yankin suka caccaki kalaman, su na mai cewa a maimakon cigaba, manufofin shugaban sun mayar da yankin arewa cibiyar talauci.

    A gefe guda kuma, gwamnatin mulkin sojan Nijar zargi Ivory Coast, Benin, Faransa, Chadi da kuma ECOWAS da  kitsa shirin kifar da gwamnati, biyo bayan wani bore da ya faru a ranakun 28 zuwa 29 ga watan Agusta, da kuma haifar da rarrabuwar kawuna, musamman a tsakanin rundunar soji.

    Yayin da ake tsaka da damana har ma aka fara tunkarar alamomin kaka, har yanzu akwai wasu garuruwa 20 na yankin Damagaram da ba su samu saukar ruwan shuka ba a Ƙaramar Hukumar Gangara na gundumar Tanut.

    Mafi yawanci damina Niger bata wuce wata 3 zuwa 4, domin dai tana ƙarewa a watan Satumba in ta yi tsawon watan Oktoba.

    Domin jin cikakken shirin, latsa alamar sauti.

    21 min
  • Adadin mutanen da suka mutu a ambaliyar ruwan Nepal na ci gaba da ƙaruwa

    Shirin ''Mu Zagaya Duniya" tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako, ya taɓo muhimman batutuwan da suka faru a makon da muke bankwana da shi, inda ya taɓo yadda ƴanbindiga suka yi awun gaba da mutum sama da 600 a wani kauye da ke kan iyakar Najeriya da Benin a can jihar Neja. Adadin mutanen da mumunar ambaliyar ruwa ta kashe a Nepal ya haura zuwa 470.

    A ɓangaren wasanni kuwa, shirin ya yi waiwaye kan rahoto murabus ɗin shugabancin hukumar kwallon kafa ta Najeriya da kuma yadda aka gudanar da bikin ranar Hausa.

    Ku latsa lamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna..........

    21 min
  • Mu zagaya Duniya: Fara yaƙin neman zaɓe da musayar yawu tsakanin Tinubu da Atiku

    Shirin ''Mu Zagaya Duniya" tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako kamar yadda aka saba ya taɓo muhimman batutuwan da suka faru a makon da muke bankwana da shi a Najeriya da sauran ƙasashen Afrika da ma duniya baki ɗaya.

    Cikin batutuwan da shirin ya taɓo akwai yakin neman zaben Najeriya, inda aka jiyo tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar na shan alwashin dawo da tallafin man fetur, da kuma raddin shugaba Tinubu kan wannan furuci, sai cikar shekaru goma sha biyar da kifar da gwamnatin shugaban Libya Muammar Ghaddafi, inda a yankin Gabas ta tsakiya muka tabo labarin Iran da ta sanya ladan makudan kudade ga duk wanda ya kamo mata sojojin Amurka dama sauran muhimman labarai daga sassa daban-daban na duniya.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    21 min
  • Waiwaye game da muhimman labarai da suka faru a wannan makon

    A Colombia, wata girgizar ƙasa mai karfin maki 7.4 da ta afkawa ƙasar da ke kudancin Amurka tare da hallaka akalla  mutane sama da 100, yayin da wasu da dama suka jikkata,a cikin shirin da ke waiwaye game da muhimman abubuwan da suka faru a makon da mu kayi ban kwana,wato Mu zagaya Duniya za ku ji irin wainar da aka tuya a wasu ƙasashe..............

    21 min
  • Saudiya, Pakistan da Turkiya sun sanar da kulla yarjejeniyar tsaro

    Ƙasashen Saudiya,Pakistan da kuma Turkiya sun sanar da kulla yarjejeniyar tsaro a tsakanin su yau juma’a a birnin Djeddah a wani yanayi da ake kara samun tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Yarjejeniyar da aka raɗa wa suna yarjeniyar Makka, ko baya ga harakar tsaro ta kuma tanadi faɗaɗa alakar da ke tsakanin ƙasashen a fanoni daban-daban.

    21 min
  • Mu Zagaya Duniya: Zafin alaƙa tsakanin Najeriya da Afrika ta kudu

    Shirin "Mu Zagaya Duniya" tare da Oumarou Sani kamar kowanne mako ya taɓo muhimman labaran da suka faru a sassa daban daban na Najeriya ciki har da zafin alaƙa tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu, kana dambarwar ma'aikatar Bogi a Najeriya sai kuma batun cika shekaru 3 da faro mulkin Soji a Najeriya sannan batun ficewar Chadi daga kotun ICC.

    Zamu soma shirin daga Najeriya inda batun kirkirar ma’aikatar Bogin  nan ta PFIPC  karkashin jagorancin  Adeniyi Adeyimi Mattew wadda ke habbaka hulda da zuba jari ta sake tayar da kura a kasar .

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    20 min

About Mu Zagaya Duniya

From the publisher's feed

Shirin Mu Zagaya Duniya na duba Wasu Muhimman Labarai da suka ja hankalin Duniya a cikin mako. Ana gabatar da shirin ne a ranar Asabar da safe a kuma maimaita ranar Lahadi da daddare.

More shows like Mu Zagaya Duniya

Dandalin Fasahar Fina-finai by RFI Hausa

Dandalin Fasahar Fina-finai

0 Listeners

Ilimi Hasken Rayuwa by RFI Hausa

Ilimi Hasken Rayuwa

0 Listeners

Kida, Al'adu da Fina-Finai by RFI Hausa

Kida, Al'adu da Fina-Finai

1 Listeners

Lafiya Jari ce by RFI Hausa

Lafiya Jari ce

0 Listeners

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare by RFI Hausa

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

0 Listeners

Wasanni by RFI Hausa

Wasanni

0 Listeners

Muhallinka Rayuwarka by RFI Hausa

Muhallinka Rayuwarka

0 Listeners

Tambaya da Amsa by RFI Hausa

Tambaya da Amsa

0 Listeners

Tarihin Afrika by RFI Hausa

Tarihin Afrika

0 Listeners