
Sign up to save your podcasts
Or


A wannan makon shirin ya yi duba kan cutar Diptheria, ko kuma mashaƙo, cutar da a baya-bayan nan ake yawan ganin ɓarkewar annobarta a wasu sassa na jihohin Najeriya wadda kuma ke kisan ɗimbin mutane baya ga kwantar da dama a asibitoci, inda wasu alƙaluma ke cewa daga watan Janairu zuwa Agustan shekarar nan mutane dubu 16 da 997 suka kamu da cutar a sassan Najeriya.
Masana sun yi ittifaƙin cewar mashaƙo ko kuma Deptheria tafi shafar yaran da ba a yiwa rigakafin cutuka ba ƴan shekara 1 zuwa 14 kodayake a wasu lokutan akan samu hatta waɗanda aka yiwa rigakafin sun kamu.
Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Goyon ciki da haihuwa na cikin mayan ƙalubalen Lafiyar da suka addabi ƙasashe masu tasowa irin Najeriya, ta yadda a kowacce rana ake ganin mutuwar ɗimbin mata a lokacin haihuwa ko kuma renon ciki, baya ga tarin jarirai da ke rasa ransu. A irin wannan yanayi galibi Ungozomar gargajiya ke matsayin masu ceto a irin wannan yanayi.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.............
Bisa ga zubin halittar ɗan adam kowacce mace kan iya haihuwa aƙalla sau 15 zuwa 30 a tsawon rayuwarta, a wani yanayi da ƙasashen Afrika ke sahun gaba wajen yawan haihuwar, kodayake liktoci na jan hankali game da muhimmancin bayar da tazara ko kuma hutu koma taƙaita haihuwar baki ɗaya saboda dalilai na lafiya.
Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.
Shirin Lafiya jari ce na wannan mako ya mayar da hankali ne kan cutar dajin mahaifa da ke addabar mata musamman a Nahiyar Afrika.
Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashi Aminu.
Shirin lafiya jari ce a wannan karon ya mayar da hankali kan ɗabi'ar shan magani ba tare da shawara ko umarnin likitoci ba, wanda a turance ake kira Self-medication da kuma illar hakan ga lafiyar jama’a.
Wasu alƙaluma sun nuna cewa fiye da kashi 70 cikin ɗari na ƴan Najeriya ne yanzu haka sun bijirewa ziyartar asibitoci ta yadda suke shan magungunan tarin cutuka ba tare da umarnin ƙwararru ba, musamman a ɓangaren cutukan da suka shafi zazzabin cizon sauro da ciwon kai da kuma tari baya ga ciwon gaɓoɓi ko ma ciwon ciki dama ciwon kunne ko ciwon haƙori da sauransu.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.............
A wannan makon shirin na Lafiya Jari ce zai yi duba ne kan lalurar Depression ko kuma damuwa mai tsanani a harshen hausa, cutar da ke ƙoƙarin zama ruwan dare tsakanin al’umma a baya-bayan nan, wataƙila ko saboda yanayi da matsin rayuwa.
Ku danna almar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.
Shirin a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya leƙa jamhuriyyar Nijar inda ya yi dubi kan yadda ake samun kafuwar wuraren saida magunguna birjik musamman a lokaci irin na damuna, wato dai lokacin da ake ganin yawaitar cutuka irin zazzaɓin cizon sabro.
Danna alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.....
A wannan makon shirin Lafiya Jari ce ya mayar da hankali kan sake ɓarkewar cutar kwalara ko kuma amai da gudawa a jihar Borno, lamarin da ya jefa ɗimbin jama’a a yanayi na matuƙar damuwa damuwa musamman bayan da rahotanni ke cewa an samu yaɗuwar annobar cutar har a yankunan da ake ajje da ɗimbin mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da matsugunansu.
A wannan makon shirin na lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba duba kan cutar Schistosomiasis (shustosumayusus) ko Bilharzia koma Snail fever kamar yadda wasu ke kiranta, cutar nan dai da aka fi sani da tsagiya a hausance, cutar alƙaluma ke nuni da cewa kashi 90 cikin 100 na masu kamuwa da ita na a nahiyar Afrika.
Shiga alamar sauti don sauraron karin bayani.......
Shirin Lafiya Jari ce na wannan mako ya yi dubi ne kan yawaitar cututtuka a irin wannan lokaci na damuna, daidai lokacin da bayanai ke nuni da cewa farashin magunguna ya yi tashin gauron zabbi.
Latsa alamar sauti don sauraren shirin tare da Azima Bashir Aminu...
From the publisher's feed
Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi,…

0 Listeners

0 Listeners

1 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners