Muhallinka Rayuwarka

Muhallinka Rayuwarka

By RFI Hausa
Download on the App Store

Muhallinka Rayuwarka episodes

  • Yadda matsalar tsuntsayen Jan Baki ta addabi manoma a jihar Jigawa

    Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan mako ya yi duba ne kan matsalar tsuntsayen jan baki da ke lalata gona komai girmanta a duk lokacin da suka durfafeta a jihar Jigawa da ke Arewacin Najeriya, wadda ta yi ƙamarin da har wasu manoma na cewa, dabarun da suka daɗe suna amfani da su wajen korar tsuntsayen sun kasa magance matsalar, lamarin da ya tilasta musu neman wasu sabbin hanyoyi.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nasiru Sani...........

    21 min
  • Hukumar NIMET a Najeriya ta yi hasashen yiwuwar ambaliya a jihoh 13 na ƙasar

    A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan duba sabon hasashen da Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya ta yi, game da yiyuwar samun matsalar ambaliyar ruwa a wasu jihohi 13 na kasar a wannan damunar.

    A baya-bayan nan, hukumar hasashen yanayi ta Nigeria wato NIMET, ta sake fito da wani sabon hasashen yiyuwar ambaliyar ruwa a cikin watan Agustan wannan shekara, tsakanin ranar 11 zuwa 20 ga watan na Agusta, a wasu jihohi 13 na kasar.

    Cikin sanarwar da ta bayar, hukumar ta NIMET, ta bayyana cewa hasashen nata, ya dogara ne kan adadin ruwan saman da ake fatan samu, da yanayin kasa tare da girman magudanan ruwa da kuma yawaitar madatsun ruwa.

    21 min
  • Matsalar ambaliyar ruwa da ake samu duk lokacin damina a ƙasashen Afrika

    Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan mako ya yi duba ne kan matsalar ambaliyar ruwa da ake fuskanta kowace shekara lokacin damina a sassan ƙasashen Afrika.

    Kamar kowace shekara, a bana ma ana hasashen samun ambaliyar ruwa a wasu kasashen yammacin Afrika, inda akan samu rasa rayuka da dukiya mai tarin yawa. A Najeriya, an sha samun hasarar rayuka a sanadin matsalar ambaliyar ruwan, da kan rutsa da wasu yankunan kasar.

    Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

    20 min
  • Yadda dazuka ke taimakawa wajan kare muhalli

    Shirin Muhallinka rayuwarka na wannnan mako tare da Nasiru Sani ya duba irin gudun mawar da ganzun daji ke bayarwa wajan kare muhalli daga matsalar  sauyin yanayi

    Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin......

    21 min
  • Yadda dazuka ke taimakawa wajan kare muhalli

    Shirin Muhallinka rayuwarka na wannan mako tare da Nasiru Sani ya duba irin gudun mawar da dazuka ke bayar wa wajan kare muhalli daga matsalar sauyin yanayi.

    Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......

    21 min
  • Illolin karancin gonaki kusa da jama'a da yadda ya shafi burin bunkasa samar da abinci

    Sau da dama, masu burin shiga harkokin noma a Nigeria kan canza tunaninsu, sakamakon rashin samun gonakin da za su noma kusa da gari, lamarin da kan tilasta su jingine aniyarsu ta yin noma.

    Gwamnatin Nigeria dai, ta sha kira ga ‘yan kasar da su koma gona, la’akari da yadda Allah ya albarkaci kasar da wadatattun filayen noma da kuma yanayi mai kyau da za a iya noma kowane irin nau’in kayan abinci.

    20 min

About Muhallinka Rayuwarka

From the publisher's feed

Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).

More shows like Muhallinka Rayuwarka

Dandalin Fasahar Fina-finai by RFI Hausa

Dandalin Fasahar Fina-finai

0 Listeners

Ilimi Hasken Rayuwa by RFI Hausa

Ilimi Hasken Rayuwa

0 Listeners

Kida, Al'adu da Fina-Finai by RFI Hausa

Kida, Al'adu da Fina-Finai

1 Listeners

Lafiya Jari ce by RFI Hausa

Lafiya Jari ce

0 Listeners

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare by RFI Hausa

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

0 Listeners

Wasanni by RFI Hausa

Wasanni

0 Listeners

Mu Zagaya Duniya by RFI Hausa

Mu Zagaya Duniya

0 Listeners

Tambaya da Amsa by RFI Hausa

Tambaya da Amsa

0 Listeners

Tarihin Afrika by RFI Hausa

Tarihin Afrika

0 Listeners