Saudiyya da wasu kasashen Duniya da suka hada da Najeriya da Nijar na gudanar da bukukuwan Idin ƙaramar Sallah bayan kammala azumin watan ramadana.
A jiya Asabar ne ,ƙotun kolin Saudiyya ta yanke hukuncin cewa yau Lahadi 30 ga Maris, 2025 ita ce ranar farko ta Idin Al-Fitr, a cewar wata sanarwa da kotun masarautar Saudiyya ta fitar ta kafafen yada labarai.
Ana dai kayyade lokacin da za a gudanar da bukukuwan, wanda ke nuna karshen azumin watan Ramadan, bisa ga ganin jinjirin wata, kamar yadda kalandar musulunci ya tsara.
Sai dai ƙasashen Oman da Jordan da ke makwabtaka da ita da kuma Iran masu rinjayen mabiya Shi'a sun ce ba za a fara sallar Idi ba har sai ranar litinin saboda har yanzu ba a ga jinjirin wata ba. Masar da sauran kasashen Arewacin Afirka sun bi sahun.
A duk fadin duniyar musulmi, shagulgulan watan Ramadan na bana ya ci tura, bayan da Isra'ila ta sake kai hare-hare a zirin Gaza, inda yakin da ta ke yi na ƙawar da ƙungiyar Hamas ya yi sanadin mutuwar dubun-dubatar mutane, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta ƙasar ta Hamas ta bayyana.