Ilimi Hasken Rayuwa

Ilimi Hasken Rayuwa

By RFI HausaEducation
Download on the App Store

Ilimi Hasken Rayuwa episodes

  • Wani matashi ya yi nasarar ƙera jirgi marar matuƙi a jihar Kano

    Shirin Ilimi Haske Rayuwa na wannan makon, ya yi dubi ne kan yadda wani matashi a jihar Kanon Najeriya ya ja hankalin jama’a, bayan ƙirƙirar jirgi maras matuƙi, daidai lokacin da matasan wannan ƙasa ke faɗi tashin yadda za su samo masu ɗaukar nauyin ayyukan fasahar da suke son cimmawa.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruwa...........

    11 min
  • Tasirin faɗowar wasu sinadarai daga sama a fagen kimiyya da fasaha

    Shirin "Ilimi Hasken Rayuwa" na wannan mako tare da Shamsiyya Haruna ya yada zango ne a Jamhuriyar Nijar inda abaya-bayan nan aka rika samun fadowar wasu abubuwa daga sararin samaniya, lamarin da ke ci gaba da faruwa a sassan a kasar.

    A baya bayan ne dai wasu abubuwa suka fado daga sararin samaniya a kauyuka 5 daban daban a yankin Kornaka, da Dakwaro da suka hada da Dan Madi, Baushi, da sauransu, haka abin ya taba kasancewa a 2021 inda aka samu wani babban dutse da ya fado daga sama a garin Aikawa na yankin Gazawa sannan, an samu wasu duwatsun a yankin Tanut, Agades da sauran yankunan Nijar.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...

    10 min
  • Ra'ayoyi sun banbanta kan amfani da fasahar AI wajen yin tiyata

    Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako a wannan makon, ya mayar da hankali kan binciken da ya gano cewa shigar fasahar AI cikin fannin tiyata na haifar da wasu matsaloli masu kama da barazana ga rayuwar ɗan adam, kan haka ne ma muka zanta da masana a fannin kimiyya da kuma ɓangaren lafiya, inda muka jiyo ra’ayoyin mutane game da yadda wasu ke yarda AI ya duba lafiyarsu har ta kai ga tiyata a wasu lokutan.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna............

    11 min
  • Yadda satar jarabawa ke taka rawa wajen kassara ingancin ilimi a Najeriya

    Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda satar jarabawa ke ƙoƙarin zama ruwan dare a makarantun sassan Najeriya, matsalar da ke ci gaba da illa ga ingancin ilimi a dukkan makarantu na ƙasar.

    Akwai zarge-zargen da ke nuna cewa wasu daga cikin jami'an hukumomin da ke kula da shirya jarabawa a matakai daban-daban na taimakawa wannan mummunar ɗabi'a ta satar jarabawa ta hanyar fallasa amsoshin tambayoyin da ake shirin fitarwa ga ɗalibai.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    10 min
  • Ana fuskantar koma bayan koyan harshen larabci a arewacin Najeriya

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako tare da Shamsiyya Haruna ya mayar da hankali ne kan dalilan da suka haddasa rashin koyon ingantaccen larabci tsakanin daliban sakandare a arewacin Najeriya, sabanin lokutan baya.

    A shekarun baya, alkaluma sun nuna cewa kusan kaso hamsin na larabcin da Dalibai ke koya suna samun sa ne a makarantun boko ba lallai sun sun halarci makarantun Arabiya, al’amarin dake neman zama tarihi a wannan zamani.

    Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......

    10 min
  • Yadda satar jarabawa da cin hanci da rashawa ke kassara ɓangaren Ilimi a Kamaru

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda wani bincike can a Jamhuriyyar Kamaru ya gano yadda satar Jarabawa da cin hanci da rashawa ke mummunan tasiri a ɓangare ilimin ƙasar.

    Matsalar ta cin hanci da rashawa kai tsaye ta yi mummunar illa ga yanayin ɗaukar malamai aiki da gina makarantu ko kuma samar da ci gaba a ɓangaren na Ilimi, yayinda a gefe guda satar jarabawar da ɗalibai ke yi ke zagon ƙasa ga makomar ilimi a ƙasar.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    10 min
  • Makomar karatu a yankin arewacin Najeriya cike da barazanar ƴanbindiga

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako tare da Shamsiyya Haruna ya mayar da hankali kan makomar karatun ɗalibai a makarantun Najeriya musamman yankin arewaci mai fama da matsalolin tsaro, dai dai lokacin da aka koma sabon zangon karatu Iyaye na cike da fargaba kan tsaro a makarantu.

    Makwanni gabanin tafiya hutun zangon da ya gabata cikin watan Nuwamban bara ne, hare-haren ƴan bindiga suka tilasta kulle makarantu a sassan arewacin Najeriyar ciki har da makarantun Unity da ke ƙarƙashin kulawar gwamnatin Tarayya.

    Wasu na da ra'ayin cewa sai an haɗa ƙarfi da ƙarfe tsakanin dukkanin ɓangarori ne, ɗalibai za su samu cikakken tsaro a makarantu tare da samun ɗorewar Ilimi a yankin.

    Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.

    10 min

About Ilimi Hasken Rayuwa

From the publisher's feed

Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken…

More shows like Ilimi Hasken Rayuwa

Labarai by RFI Hausa

Labarai

0 Listeners

Kasuwanci by RFI Hausa

Kasuwanci

0 Listeners

Muhallinka Rayuwarka by RFI Hausa

Muhallinka Rayuwarka

0 Listeners

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare by RFI Hausa

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

0 Listeners

Lafiya Jari ce by RFI Hausa

Lafiya Jari ce

0 Listeners

Wasanni by RFI Hausa

Wasanni

0 Listeners

Dandalin Fasahar Fina-finai by RFI Hausa

Dandalin Fasahar Fina-finai

0 Listeners

Tarihin Afrika by RFI Hausa

Tarihin Afrika

0 Listeners

Al'adun Gargajiya by RFI Hausa

Al'adun Gargajiya

0 Listeners

Tambaya da Amsa by RFI Hausa

Tambaya da Amsa

0 Listeners