
Sign up to save your podcasts
Or


Shirin ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya duba yadda wasu manoma a Najeriya, musamman arewacin kasar ke hana yaransu zuwa makaranta, har sai an yi girbin amfanin gona, saboda wasu dalilai
Ku shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.....
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda bikin yaye ɗalibai da ɗabi'ar rubutu a jikin rigunan juna dama sauran shagulgulan da akanyi a bikin na kammala makaranta ke taka muhimmiyar rawa wajen lalata tarbiyyar ɗalibai.
Tsawon shekaru aka ɗauka wannan dabi'a na ciwa iyaye tuwo a ƙwarya dama sauran masu ruwa da tsaki a ɓangaren tarbiyyar al'umma.
Sai dai bayan tsanantar ƙorafe-ƙorafe kan wannan ta'ada, kwatsam an wayi gari gwamnatin jihar Kaduna ta yi uwa da makarɓiya wajen haramta irin bukukuwan har ma da wasu ƙarin dokoki da suka shafi sashen na ilimi ciki har da haramtawa makarantu ƙarin kuɗin makaranta.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.
Shirin na wannan rana zai ɗora kan wanda muka gabatar muku a makon jiya game da karancin malamai a makarantun jihar Jigawa ta arewacin Najeriya.
Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nura Ado Sulaiman.
Shirin ilimi Hasken rayuwa na wannan rana ya mayar da hankali ne kan tsarin koyarwa da Nijar ke yi na baiwa dalibai karin horaswa akan darussa masu wahala a lokutan hutu.
Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nura Ado Sulaiman.
Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan mako ya duba matakin gwamnatin Najeriya na dakatar da kafa makarantun gaba da sakandare a fadin ƙasar har na tsawon shekaru 7, mataakin da ya biyo bayan wani zama da majalisar zartaswar ƙasar ta yi a ƙarƙashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu. Majalisar ta ce babu amfanin kafa makarantun da ba za a samu abin da ake buƙata ba, a maimakon haka zai kyautu a inganta waɗanda ake da su.
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda wasu daga cikin Makarantun Firamare a jihar Kano suka koma koyarwa da harshen Hausa da nufin sauƙaƙa koyo da koyarwa tsakanin yaran jihar.
Kafin yanzu dai akwai dokar da ta soke koyarwa da harsunan gida 3 a Makarantun Najeriyar da suka ƙunshi Hausa da Yarabanci da kuma Igbo, inda tuni aka ga yadda wasu Makarantu suka daina koyarwa da wannan harshe, kodayake tun tuni dama yankin kudancin Najeriya ya yi watsi da wannan doka tare da ci gaba da koyar da harsukan.
Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.
Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon zai duba tsarin cigaban manyan malaman jami'a a Jamhuriyar Nijar, wanda ke kai su ƙololuwa a harkar ilimi.
Domin samun ingataccen ilimi, dole ne a samu ƙwararrun malamai da za su koyar da ɗalibai da ke karatu a fannoni dabam-dabam. haka zalika malaman da ke koyarwar su ma su na neman hanyoyin ƙara ƙwarewa don kai wa ƙololuwa a aikin na su na koyarwa.
Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' a wannan makon ya mayar hankali ne akan makomar amfani da harshen uwa a makarantun Najeriya, inda ya yi dubi da cigaba da kuma akasi. Masana dai sun tofa albarkacin bakinsu akai.
Tun bayan da gwamnatin Najeriya ta shelantar fara amfani da harshen uwa wajen bayar da ilimi musamman a matakin farko, masana da masharhanta suka fara sharhi kan ƙalubalen da shirin zai iya fuskanta idan aka fara aiwatar da shi.
A Najeriya dakatar da tallafin ciyarwa da gwamantocin ƙasar suka yi a Makarantun wasu sassan ƙasar musamman arewaci ta haifar da ƙafar Ungulu ga himmar zuwa makarantu a tsakanin ɗalibai da Iyayensu.
Wasu Iyaye da aka zanta dasu sun ce shirin tallafin na taka muhimmiyar rawa wajen sama musu sassauci wajen ciyar da 'ya'yan nasu, amma daga bisani aka ci karo da tsaiko.
Sai a latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiya Haruna.
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali ne kan tasirin da Makarantar koyar da harshen Larabci ta ASA a Kano ta yi wajen yaye fitattun mutane a matakai daban-daban musamman a ɓangaren shari'a kodayake Makaranta na fuskantar koma baya a yanzu.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.
From the publisher's feed
Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken…

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners