
Sign up to save your podcasts
Or


Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya tattauna da Farfesa Aminu Bello Usman daga Birtaniya, ɗan jihar Kano da ke tarayyar Najeriya, wanda ya ƙirƙiri wata Manhaja da za ta taimaka wa mutane wajen sauƙaƙa musu lisaffin hada-hadar kuɗaɗe musamman ma na haraji.
Wani abin ban sha’awa dangane da Manhajar da aka fi sani da Software a Turance, shi ne yadda wannan manhajar ta ƙunshi harsuna biyar.
Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nasir Sani.
Mutane da suka tsinci kansu a cikin masu buƙata ta musamman sakamakon nau’ikan nakasar da suka fama da ita sun share shekaru suna fuskantar giɓi babba a muhimman fannonin rayuwa daban daban, ciki kuwa har da samun guraben ayyukan yi ko da kuwa a ce sun yi katarin tsallake shingen samun ilimi, matsalar da ta fi ƙamari a ƙasashe masu tasowa ciki har da na Nahiyar Afrika.
Mutane da suka tsinci kansu a cikin masu buƙata ta musamman sakamakon nau’ikan nakasar da suka fama da ita sun share shekaru suna fuskantar giɓi babba a muhimman fannonin rayuwa daban daban, ciki kuwa har da samun guraben ayyukan yi ko da kuwa a ce sun yi katarin tsallake shingen samun ilimi, matsalar da ta fi ƙamari a ƙasashe masu tasowa ciki har da na Nahiyar Afrika.
Kan wannan batu shirin Ilimi Hasken rayuwa na wannan lokaci zai tattauna, bayan da ya yi tattaki zuwa Jihar Jigawa da ke tarayyar Najeriya, akan ƙorafin da wasu fama da nakasar suka yi a bisa ganin cewar suna neman rasa damar samun guraben ayyukan yi da suka cancanci dafewa.
A latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.
Shirin ilimi Hasken rayuwa na wannan mako dubi ne kan yadda makarantu masu zaman kan a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya, suka fara ɗaukar matakin kai ƙarar iyayen yara gaban hukumomi, sakamakon rashin biyansu kuɗaɗen karatun ƴaƴansu na tsawon lokaci.
Abin damuwar shine, idan iyayen suka tara kuɗin makaranta har ya kai matakin da ba za su iya biya ba, sai su sauya wa yaran nasu wurin makarantu, kenan wancan kuɗi da ake binsu ya bi ruwa.
Babbar matsalar ita ce, wannan al’amari a wasu lokutan ya kan haifar da ƙalubale ga ɓangarorin da ke gudanar da irin wadannan makarantu, abin da har ke kaiwa ga rufewa ko kuma sayar da makaranta, saboda rashin isassun kuɗin da za su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna..........
A wannan makon, shirin yayi dubi ne kan batun yadda har kawo yanzu ake samun malaman makaratu masu zaman kansu a Najeriya dake ɗaukar albashin Naira dubu 15 zuwa sama, maimakon mafi ƙaranci albashin naira dubu 70 da gwamnati ƙasar ta yi dokar biya.
Duk da irin kuɗaden da ake shatawa iyayen yara, har ta kai idan yaronka ba a biya mishi kuɗin makaranta ba, to kuwa za a kora maka shi gida, hakan be sanya sun inganta albashin malaman ba.
Makaranta mai zaman kanta mutum ke kafa ta ko haɗin gwiwa na wasu mutane domin taimakawa ko ba gudunmawa yayin da a wannan lokaci da dama sun mayar da ita matsayin kasuwanci, abin da masana ke ganin kenan akwai buƙatar Malamai su samu yanayi mai kyau da walwala wanda ta hakanne zasu samu ƙwarin gwiwa wajan bayar da ilimi mai nagarta.
Hauwa'u Adam dake koyarwa a wata Makarata dake yankin Jambulo a jihar Kanon Najeriya, ta sheda mana cewa saboda karatunta yakai matakin digiri ne ake biyanta Naira dubu 20, amma masu kwalin babbar difloma ta HND da NCE albashin daga dubu 17 ne zuwa 18
Masana da masu fashin baki na ganin cewa, gwamnatoci sun yi sakaci sosai, musamman ta hanyar sakarwa makarantu masu zaman kansu linzami suna abin da suka ga dama, idan kaji mahukunta na kai ruwa rana da su to kuwa baya wuce akan haraji ne.
A wannan makon shirin ya karkata akala ne kan makomar ilimi a Najeriya, inda hukumomi suka fara rufe makarantu saboda matsalolin tsaro da ke neman dakushe makomar ilimin manyan gobe. Me yasa jihohi ke gaggawar rufe makarantu bayan sace ɗalibai a Kebbi da Niger a kwanan nan? Shin babu wasu hanyoyin kawo ƙarshen matsalar tsaro sai dai rufe makarantu?
Tambayar kenan da ‘yan Najeriya ke yiwa gwamnatin ƙasar, yayin da ake ganin tarin jami’an tsaro na yiwa masu rike da manyan makamai rakiya, abin da ke nuna yawan jami’an tsaron da ƙasar ke da shi idan aka haɗa ƴansanda da sojoji da jami’an tsaron Civil Defence da sauransu, to kuwa iyaye suka ce idan har aka yi la’akari da wannan za a iya samarwa ɗalibai tsaro.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.........
Shirin a wannan mako, kareshe ne kan maudu’in da muka tattaunawa a makonni biyun da suka gabata, wanda ya mayar da hankali kan yadda rubutun Ajami a kasar Hausa ya yi shura, da kuma yadda yake neman bacewa a wannan zamani.
Yayin da ake ganin har yanzu a Jamhuriyar Nijar, akwai yankunan da suke amfani da ajami wajen isar da sakonni, Malaman tsangaya daga Najeriya ma suna amfani da wannan tsarin rubutu wajen musayar bayanai a tsakaninsu.
Yaɗuwar addinin Islama a Ƙasar Hausa masana suka ce, ya taimaka sosai wajen shaharar wannan salo na rubutu, sannan kuma ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen inganta hanyoyin sadarwa na wancan lokaci.
A tattaunawarmu da masanin tarihi daga Kanon Najeriya, farfesa Tijjani Naniya, ya bayyana cewa, zuwan turawan mulkin mallaka, shine musabbabin gushewar wannan rubutu a kasar Hausa, amma a wancan lokaci, rubutun na ajami ya ci kasuwa tsakanin masana, malamai, sarakuna da kuma ‘yan kasuwa.
Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya cigaba ne da mayar da hankali kan makomar rubutun Ajami a ƙasar Hausa, nau'in rubutun da ya taimaka matuƙa wajen musayar bayanai tsakanin al'ummar Hausawa tun gabanin zuwan Turawan mulkin mallaka.
A shekarun baya-bayan nan rubutun na Ajami ya zama tarihi a ƙasar Hausa bayan da kowanne ɓangare ya rungumi tsarin boko daga turawan Yamma.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin kashi na biyu:
Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan makomar rubutun Ajami a ƙasar Hausa, nau'in rubutun da ya taimaka matuƙa wajen musayar bayanai tsakanin al'ummar Hausawa tun gabanin zuwan Turawan mulkin mallaka.
A shekarun baya-bayan nan rubutun na Ajami ya zama tarihi a ƙasar Hausa bayan da kowanne ɓangare ya rungumi tsarin boko daga turawan Yamma.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali ne kan dokar da ta tilastawa makarantu masu zaman kansu rage kudin makaranta da gwamnatin Nijar ta kafa, wanda ke zuwa bayan ƙarin hutun makarantu na makwanni biyu saboda mamakon ruwan a ƙasar ta yankin Sahel.
Ƙarƙashin wata doka da shugaban gwamnatin Sojin Nijar Abdourraham Tchiani ya sanya hannu ce ta buƙaci dukkanin makarantun su rage kuɗin da suke karɓa da kashi 20, kodayake wannan doka bata shafi makarantun da ke karɓar kuɗin da bai kai CFA jaka hamsin ba.
Tuni iyaye suka yi maraba da wannan mataki.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan makon ya mayar da hankali kan gudunmawar malaman makaranta ga rayuwar jama'a dai dai lokacin da aka gudanar da bikin ranar Malamai a sassa daban-daban na duniya.
Majalisar Ɗinkin Duniya ce ta ware wannan rana da nufin girmama gudunmawar da malaman ke bayarwa, sai dai an gudanar da wannan rana ne a dai dai lokacin da malamai a Najeriya dama sauran ƙsashen Afrika ke ganin ƙololuwar matsin rayuw sakamakon matsalolin da suka dabaibaye su kama daga rashin kyawun yanayin aiki dama ƙarancin albashi.
Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin...
From the publisher's feed
Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken…

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners