Ilimi Hasken Rayuwa

Ilimi Hasken Rayuwa

By RFI HausaEducation
Download on the App Store

Ilimi Hasken Rayuwa episodes

  • Ghana ta fara wani yunƙuri inganta tsarin koyo da koyarwa da binciken Likitanci

    Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako, shirin da bisa al'ada ke taɓo batutuwan da suka shafi ilimin kimiyya da fasaha ko ƙere ƙere, baya lalubo ƙalubale ko kuma ci gaban da waɗannan fannoni suka samu.

    A wannan makon, shirin ya yada zango a Ghana inda zakuji yadda mahukuntan Ghana suka bullo da wani matakin inganta ilimin likitoci bayan miƙa cibiyar kimiyya da Fasaha ga babbar Jami'ar ƙasar, wanda zai taimaka wajen binciken kimiyya da fasaha.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    10 min
  • Tasirin makarantar koyar da harshen Larabci ta SAS ga Arewacin Najeriya

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali ne kan tasirin da Makarantar koyar da harshen Larabci ta ASA a Kano ta yi wajen yaye fitattun mutane a matakai daban-daban musamman a ɓangaren shari'a kodayake Makaranta na fuskantar koma baya a yanzu.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    11 min
  • Muhimmancin kai ziyarar buɗe ido ta Ilimi ga Ɗalibai

    Shirin Ilimi Hasken Tayuwa na wannan makon tare da Nura Ado Suleiman ya yi duba a kan Muhimmancin yin tattaki ko kuma Ziyarar Ilimi Da Makarantu Ke Shirya Wa ‘Dalibai lokaci zuwa lokaci da wayar musu da kai ko ƙara musu ilimi a kan muhimman batutuwa.

    Latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin......

    10 min
  • Dalilan da ya sa masana ke neman a yi taka tsan-tsan wajen amfani da fasahar AI

    Shirin Ilimi na wannan mako ya yi duba ne kan muhawarar da ake ci gaba da tafkawa kan fasahar nan ta kimsawa na’ura irin basirar ɗan Adam wadda aka sani da AI, wasu masana dai na cigaba da gargaɗin cewa ya zama dole a yi taka tsan-tsan domin bai kamata a saki jiki da wannan Fasaha ta AI ba, duk da amfanin da ta ke tattare da ita wajen sauƙaƙa ayyuka masu wahala da ɗan Adam ke yi.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Shamsiyya Haruna.................

    10 min
  • Yadda faɗuwar jarabar JAMB ta shafi ɗalibai da ke neman gurbin ƙaratu a Najeriya

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako ya yi duba ne kan matsalar da aka samu ta faɗuwar jarabar sharar fage ta shiga jami'o'in Najeriya JAMB, da hukumar shirya jarabawar ta ce hakan ya faru ne a sakamakon tangarɗar da aka samu ta na'ura a lokacin rubutawa. Matslar da ta hana shafi ɗalibai dubu 300 da suka rubuta jarabawar. 
     

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.........

    11 min
  • Yadda Malaman makarantu suka tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a Abujan Najeriya

    Shirin na wannan mako ya ba da hankali ne kan bikin ranar yara ta duniya wanda aka saba gudanarwa a ranar 27 ga watan mayun kowacce shekara, a Najeriya yayin da ake bikin wannan rana Malaman Makarantun firamare a Abuja babban birnin ƙasar ne ke shiga watanni na uku da fara yajin aikin sai Baba ta gani, sakamakon rashin fara aiwatar da sabin tsarin mafi ƙarancin albashi na naira dubu 70 kamar yadda ƙungiyarsu ta Malaman makarantu ta bayyana. lamarin da ya ta da yajin aikin gargaɗi a baya kafin su tsunduma cikin wanda suke kai a yanzu.

    10 min
  • Shirin gwamnatin Najeriya na dawo da tsarin koyarawa da harshen uwa

    A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan, shawarar gwamnatin tarayyar Najeriya ta dawo da tsarin amfani da harshen uwa a makarantun firamare da ke fadin kasar.

    Tsarin amfani da harshen uwa a makarantun firamare, wani tsari ne da aka gabatar a shekarar 2022, wadda ke da nufin inganta amfani da harsunan uwa a matsayin harshen koyarwa a makarantun firamare. Sai dai, a wancan lokaci da aka kaddamar da manufar za a yi amfani da ita ne akan Yara yan aji daya zuwa na makarantun firamare.

    Hakan kuwa ya biyo bayan bincike-bincike da aka gudanar wanda ya nuna cewa rashin fahimtar darusan da ake koyarwa da harshen Ingilishi ya bada gudunmowa wajen barin Yara makaranta da kuma haifar da koma-bayan ilimi a Najeriya.

    Sai da masana sun bayyana wasu ƙalubale da za a iya fuskanta da suka hadar da rashin wadatattun kayan koyarwa, da matsalolin zabar babban yare a cikin al'ummomi da ke amfani da harsuna da yawa.

    11 min
  • Ɓangaren ilimin wasu jihohin Najeriya sun gaza samun tallafin gwamnatin ƙasar

    Shirin na wannan mako ya duba dalilan da suka sanya bangaren ilimi a matakin farko a Najeriya na matakin jihohi ya gaza samun gajiyar tallafin da zai taimaka wajen bunkasa karatun kananan yara, duk da makudan kudaden da gwamnatin ƙasar ta ware a matsayin tallafi.

    Bisa ga kididdigar da aka yi a baya-bayan nan, akwai yara fiye da miliyan 10 da ya kamata a ce suna makaranta a Nigeria amma a halin yanzu yawo su ke yi loko-loko ba tare da samun kowani irin nau’in ilimi ba.

    ‘Yan kalilan din da suke samun halartar makaranta, mafi yawan su na fama da rashin wadatattun kayan karatu, kama daga azuzuwa, kayan koyarwa, kujeru da kuma uwa uba kwararrun malamai.

    11 min

About Ilimi Hasken Rayuwa

From the publisher's feed

Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken…

More shows like Ilimi Hasken Rayuwa

Labarai by RFI Hausa

Labarai

0 Listeners

Kasuwanci by RFI Hausa

Kasuwanci

0 Listeners

Muhallinka Rayuwarka by RFI Hausa

Muhallinka Rayuwarka

0 Listeners

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare by RFI Hausa

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

0 Listeners

Lafiya Jari ce by RFI Hausa

Lafiya Jari ce

0 Listeners

Wasanni by RFI Hausa

Wasanni

0 Listeners

Dandalin Fasahar Fina-finai by RFI Hausa

Dandalin Fasahar Fina-finai

0 Listeners

Tarihin Afrika by RFI Hausa

Tarihin Afrika

0 Listeners

Al'adun Gargajiya by RFI Hausa

Al'adun Gargajiya

0 Listeners

Tambaya da Amsa by RFI Hausa

Tambaya da Amsa

0 Listeners