Ilimi Hasken Rayuwa

Ilimi Hasken Rayuwa

By RFI HausaEducation
Download on the App Store

Ilimi Hasken Rayuwa episodes

  • Gasar HIFEST karo na bakwai a Najeriya

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako, ya yi duba ne, kan yadda wata kungiya a Najeriya, ke karfafa gwiwar daliban sakandire kan yadda za su bayyana baiwar da suke da ita, musamman a bangaren ilimin fasaha.

    11 min
  • Tasirin da salon koyarwa ke da shi wajen baiwa ɗalibai ingantatcen ilimi

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan mako, ya tattauna ne a kan salon koyarwa tun daga matakin makarantu na ƙasa wato ‘Method of Teaching’ a turance, da tasirin da wannan salo ke da shi kan bayar da ilimi. Salo ko kuma dabarun koyarwa matakai ne ko tsarin da malamai ke amfani da su wajen koyar da ɗalibai darussa, a kuma tabbatar da cewa ɗaliban sun fahimci darasin da ake yi musu.

    A mafi yawan lokuta waɗannan dabaru sukan bambamta a tsakanin darussa, zalika ya danganta da matakan ilimi daga ƙasa, da na tsakiya zuwa na sama.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman.......

    11 min
  • Gwamnatin Bauchi na shirin mayar da yara fiye da miliyan 1 makarantu

    Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda gwamnatin jihar Bauchi a Najeriya ke yunƙurin mayar da yara fiye da miliyan guda makaranta a wani yanayi da ake ganin ƙaruwar yaran da basa zuwa makaranta a yankin arewacin kasar.

    Tuni masu ruwa da tsaki a wannan yanki suka yi maraba da matakin gwamnatin ta Bauchi, lura da yadda yunƙurin zai taimaka matuƙa wajen rage ɗimbin yaran da ke gararamba ba tare da zuwa makaranta ba a Arewacin na Najeriya.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...

    10 min
  • Ɓanagrorin ilimi sun koka da matakin JAMB na durkusar da harshen Faransanci

    Sannu a hankali darussan nazarin harshen faransanci na kara karbuwa a manyan makarantun Nigeria, sai dai kuma, wani matakin da hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta JAMB a Nigeria, ta aiwatar, na cire takardar shaidar share fagen shiga jami’a ta karatun  harshen faransanci, daga cikin darussan da hukumar ta JAMB ke bayar da guraben karatunsu a manyan makarantu ya daga hankalin masu ruwa da tsaki.

    10 min
  • Yadda jami’o’i a Najeriya ke neman tallafin inganta ƙirƙirarriyar fasaha ta AI

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya duba yadda wasu manyan jami’o’i a Najeriya ke neman tallafin ƙasashen da suka ci gaba kan yadda za a inganta ƙirƙirarriyar fasaha ta AI. Tuni kuma suka gabatar da wannan buƙata tasu a wajen taron da ƙungiyar bunkasa ilimi ta ƙasashen Turai kan shirya duk shekara, inda a wannan shekara Faransa ta karbi baƙuncin irin wannan taro da ya samu halartar jami'oi 6 da aka zabo daga Najeriya.
     

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.......

    10 min
  • Yadda ake ƙara samun yawaitar masu karatun yaƙi da jahilci a Adamawa

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya tattauna ne akan yadda makarantun manya ko kuma na yaƙi da jahilci kamar yadda akan kira su, ke fuskantar ƙalubalen ɗauka ko ilimantar da ɗaliban da yawansu ke ƙaruwa a kullum, adadin da ya zarta na makarantun manyan da ake da su.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Aisha Shehu Kabara......

    10 min

About Ilimi Hasken Rayuwa

From the publisher's feed

Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken…

More shows like Ilimi Hasken Rayuwa

Labarai by RFI Hausa

Labarai

0 Listeners

Kasuwanci by RFI Hausa

Kasuwanci

0 Listeners

Muhallinka Rayuwarka by RFI Hausa

Muhallinka Rayuwarka

0 Listeners

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare by RFI Hausa

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

0 Listeners

Lafiya Jari ce by RFI Hausa

Lafiya Jari ce

0 Listeners

Wasanni by RFI Hausa

Wasanni

0 Listeners

Dandalin Fasahar Fina-finai by RFI Hausa

Dandalin Fasahar Fina-finai

0 Listeners

Tarihin Afrika by RFI Hausa

Tarihin Afrika

0 Listeners

Al'adun Gargajiya by RFI Hausa

Al'adun Gargajiya

0 Listeners

Tambaya da Amsa by RFI Hausa

Tambaya da Amsa

0 Listeners