Ilimi Hasken Rayuwa

Ilimi Hasken Rayuwa

By RFI HausaEducation
Download on the App Store

Ilimi Hasken Rayuwa episodes

  • Hukumar JAMB ta shirya taro kan bai wa naƙasassu dama

    Shirin namu na wannan mako zai yi dubi ne kan yadda  hukumar kula da harkar jarabawan shiga jami’o’i a  Najeriya wato JAMB da hadin guiwan kungiyar zabiya na kasa ta shirya taron nahiyar Afrika na farko kan baiwa nakasassu ko masu larura ta musamman dangane da  harkar ilimi kamar kowani dan adam.

    Taron an shirya shi ne dai la’akari da irin kalubalen da masu larura ta musamman ke fama da ita a kasashe masu tasowa kamar Najeriya,kama daga kyama,nuna musu banbanci da dai sauransu.

    10 min
  • Fannin ilimi a Najeriya na fuskantar barazana sakamon matsin tattalin arziki

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya yi duba ne a kan yadda matsin tattalin arziki da kuma tsare-tsaren gwamnati suka kassara fannin ilimi a tarayyar Najeriya. Daga ɓangaren mahukunta jami'o'in suna ganin tsare-tsaren da gwamnati ta bullo da su a fannin ilimi sune suka sanya a wannan lokaci ko da gyare-gyare a jami'o'in basa iya aiwatarwa.

    Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin tare da Aisha Shehu Kabara........

    11 min
  • Tsarin ilimin Sakandire kyauta a Ghana ya ƙarfafa gwiwar dubban ɗalibai

    Shirin ilimi hasken rayuwa tare da Aisha Shehu Kabara a wannan makon ya mayar da hankali kan tsarin bayar da ilimin Sakandiren kyauta a Ghana, wanda ya taimaka matuka wajen ƙara yawan Ɗaliban da ke halarta karatu a wannan mataki.

    Duk da cewa shirin ya laƙume kuɗaɗe masu tarin yawa amma gwamnatin ƙasar ta Ghana ta ce ko shakka babu kwalliya ta biya kuɗin sabulu cikin shekaru 5 da fara tsarin.

    Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shiri.

    10 min
  • Tasirin da shirin gwamnatin Ghana na ilimin sakandare kyauta ya yi

    Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa'  na wannan makon zai yi duba ne kan shirin bayar da ilimin sakandare kyauta da gwamnatin Nana-Akufo Addo ta ƙasar Ghana ta bullo da shi. Bincike ya nuna cewa wannan shiri ya yi tasiri, duba da yadda aka samu ƙaruwar adadin ɗaliban da ke karatun sakandare a cikin shekaru biyar da suka gabata. Shirin ya tattauna da masu ruwa da tsaki a wannan faannin, inda suka fayyace bayanni filla-filla a kai. 

    11 min
  • Yadda tsarin koyo da koyarwa a karni na 21 ke saukakawa wurin fahimtar karatu

    A wannan mako, shirin ya yi duba ne a kan tsarin dabarun koyo da koyarwa a ƙarni na 21 da ake kira da 21st Century Learning Skills a turance.Tsarin dabarun koyo da koyarwa na ƙarni na 21, an soma amfani da shi tun a shekarar 2001 domin zamanantar da tsarin yadda ake koyarwa ta hanyar samar da dabarun zamani da za su taimaka wa malamai wurin fahimtar da ɗalibai, sannan ɗalibai su ma su ji sauƙin fahimtar abin da ake koyar da su a aji.

    A wannan mako, mun dubi yadda tsarin yake aiki tare yadda ya sauƙaƙa wa malamai da ɗalibai wurin fahimtar karatu a wannan zamani musamman a ƙasashe masu tasowa irin Najeriya.

    Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraren shirin....

    10 min
  • Karuwar matasan da basa zuwa makaranta a Ghana

    Shirin na wannan mako ya mayar da hankali ne kan karuwar matasan da basa zuwa makaranta a Ghana.

    Hukumar kididdiga ta kasar GSS ta gano cewa kusan matasa miliyan biyu ne ba sa karatun Boko ko aikin yi ko kuma samun horon sana'o'in dogaro da kai.

    Ku danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdulkadeer Haladu Kiyawa.

    10 min
  • Yadda tsadar lantarki ke kassara harkokin karatun manyan makarantun Najeriya

    A wannan mako, shirin ya mayar da hankali ne kan yadda tsadar kuɗin wutar lantarki ke gurgunta harkokin karatu a manyan makarantun Najeriya.

    Kamar yadda aka sani, harkokin gudanarwar yau da kullum na manyan makarantu ba za su taɓa yiwu wa yadda ya kamata ba, muddin babu ingantacciyar wutar lantarki.

    To sai dai, baya ga rashin tsayayyiyar wutar a kusan manyan makarantun Najeriya, wata matsalar kuma ita ce ta tsadar wutar a sakamakon ƙarin farashin kuɗin wutar lantarki da gwamnatin ƙasar ta yi.

    Wannan dalili ne ya sanya ƙungiyar shugabannin jami’o’in Najeriya, ta yi kashedin cewa jami’o’in tarayyar ƙasar aƙalla 52 ka iya durƙushewa nan ba da jimawa ba, a sakamakon tsadar kuɗin wutar.

    Shugabannin Jami’o’in na Najeriya, sun yi wannan gargaɗi ne bayan wani sabon ƙari na kashi 300 da aka yi musu a kwanakin baya.

    Kuna iya latsa alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin...

    10 min
  • Yadda ayyukan ƴan ta'adda suka kassara harkokin Ilimi a Arewacin Najeriya

    A wannan mako, shirin ya yi duba ne a kan yadda hare-haren ‘yan ta’adda suka kassara harkokin ilimi a arewacin Najeriya, shekara 10 kenan da 'yan ta'adda suka fara kai hari kan makarantu a Najeriya, lamarin da ya fara faruwa a shekarar 2014 a makarantar sakandaren ‘yan mata ta garin Chibok da ke jihar Borno a Arewa maso gabashin kasar.

    Bincike ya nuna cewa, tun bayan harin na 2014, 'yan ta'adda sun ci gaba da kai makamancinsa a kimanin makarantu 17, waɗanda suka haɗa da makarantun Firamare da sakandare da ma manyan makarantun gaba da sakandare, inda suka yi garkuwa da dalibai da dama, an sako wasu bayan biyan kuɗin fansa, wasu kuwa suna rike a hannunsu  har zuwa yanzu. 

    Cikin shekaru goma da fara ƙaddamar da irin wannan ta'addanci kan makarantu da ɗalibai, masana sun bayyana shakku kan gwamnatin Najeriya tare da zarginta da nuna halin ko in kula kan ilimi tare da rayukan al'ummar kasar musamman ɗalibai. 

    Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin...

    10 min

About Ilimi Hasken Rayuwa

From the publisher's feed

Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken…

More shows like Ilimi Hasken Rayuwa

Labarai by RFI Hausa

Labarai

0 Listeners

Kasuwanci by RFI Hausa

Kasuwanci

0 Listeners

Muhallinka Rayuwarka by RFI Hausa

Muhallinka Rayuwarka

0 Listeners

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare by RFI Hausa

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

0 Listeners

Lafiya Jari ce by RFI Hausa

Lafiya Jari ce

0 Listeners

Wasanni by RFI Hausa

Wasanni

0 Listeners

Dandalin Fasahar Fina-finai by RFI Hausa

Dandalin Fasahar Fina-finai

0 Listeners

Tarihin Afrika by RFI Hausa

Tarihin Afrika

0 Listeners

Al'adun Gargajiya by RFI Hausa

Al'adun Gargajiya

0 Listeners

Tambaya da Amsa by RFI Hausa

Tambaya da Amsa

0 Listeners