Ilimi Hasken Rayuwa

Ilimi Hasken Rayuwa

By RFI HausaEducation
Download on the App Store

Ilimi Hasken Rayuwa episodes

  • Yadda dalibai ke barin karatu a Nijar don tafiya neman kudi a wasu kasashe

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan lokacin ya yi duba ne kan yadda dalibai da dama a Jamhuriyar Nijar, musaman maza ke barin karatu da sunan tafiya neman kudi, kasashen ketare kamar Libiya, Aljeriya ko kuma hako zinare a kasar Mali kai harma da kokarin tsallakawa Turai, abin da ya sanya kungiyoyin dalibai a kasar bazama aikin wayar da kan matasa kan sanin muhimmancin da ilimi ke da shi.

    A Nijar kashi 25 na yara ne ke samun zuwa makarantar boko, kuma daga yara 100 da ake sanyawa a makarantun firamare uku kadai ke kaiwa matakin jami’a.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna........

    11 min
  • Yadda gwamnatin jahar Neja ta fara horas da dalibai sana'oin dogaro da kai

    Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon zai yi duba ne kan yadda gwamnatin jahar Neja da ke Arewacin Najeriya, ta samar da shirin horas da dalibai sana'oin hannu don dogaro da kai. Gwamnatin jahar dai ta ware ranar Juma'ar kowane mako don gudanar da darasin koyon sana'oin hannu.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna........

    11 min
  • Yadda amfani da komfuta ya shafi kyaun rubutun dalibai

    A wannan makon zamu duba yadda ci gaban kimiyya da Ilimi ke zama wani nau’I na koma baya musamman a tsakanin dalibai a Najeriya.
    Tun bayan samar ko kuma kirkirar na’urar kwamfuta a 1837, da kuma shigowar ta Najeriya karon farko a 1963 sannu a hankali take bazuwa tsakanin jama’a, yayi da kuma ake samun ci gaba ta fannin amfani da ita.

     

    10 min
  • Gwamnatin Neja na shirin farfado da tsarin karatun makiyaya

    Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon zai yi duba ne da tsarin karatun 'yayan makiyaya, wato Nomadic Education. Gwamnatin jihar Neja ce ta yi hobbasa don farfado da shirin karatun 'yayan makiyaya a jihar. Shirin zai bai wa makiyaya damar samun ilimi a duk inda suka yi balaguro don inganta makomarsu. Yanzu haka dai shirye-shirye sun yyi nisa a game dfdaa wannan shirin a jihar Neja  mai fara da matsalar tsaro sakamakon ayyukan 'yan bindiga da ke kashe mutane da satar su don kudin fansa.

    10 min
  • Taimakon da kirkirarren Tabarau ke bai wa masu fama da matsalar raunin gani

    Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon tare da Shamsiyya Haruna ya maida hankali ne kan nazarin da masana kimiya suka yi wajen kirkirar Tabaraun hangen nesa, don taimakawa masu raunin gani. A jamhuriyar Nijar, matsalar gani na zama babban kalubale ga al'ummar kasar wacce a yanzu har aka fara samunta a tsakanin matasa.

    Tuni dai matsalar ta sanya likitoci fara kiraye-kiraye ga al'umma da su tashi tsaye wajen kula da lafiyar idonsu.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin......

    11 min
  • Iyayen dalibai a Nijar na kokawa kan tsadar kudin karatu

    Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon tare da Shamsiyya Haruna ya maida hankali ne kan yadda iyaye ke kokawa a jamhuriyar Nijar kan tsadar kudin karatun 'ya'yansu, masamman makaruntu masu zaman kansu saboda matsaloli na tsadar rayuwa da aka shiga tun bayan da sojoji suka yi juyin mulki.

    11 min
  • Najeriya: Yadda tsadar man fetur ke ci gaba da yin tasiri kan harkar ilimi

    Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan mako tare da Shamsiyya Haruna ya maida hankali ne  kan yadda matsalar tsadar man fetur ke ci gaba da yin tasiri akan harkar ilimi a Najeriya, wanda tun bayan sanar da janye tallafin mai a kasar kanana da manyan makarantu ke daukan matakai daban daban da zummar daidaita harkokinsu a cikin wannan yanayi. 

    Daga cikin wadannan matakai, wasu manyan makarantun musamman jami'o'i sun takaita ranakun zuwan aikin malamai tare da tsawaita lokutan darrusan dalibai.

    11 min
  • Tsarin koyar da ilimin Computer ga daliban da ke shirin shiga jami'a a Nijar

    Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan tasirin ilimin fasahar na'ura mai kwakwalwa ko kuma computer ga daliban da ke shirin shiga jami'a a Jamhuriyyar Nijar, sabon tsarin da aka bijiro da shi da nufin taimakawa tarin daliban da basu da gogewa a fannin na fasahar na'urar computer.

    Wannan mataki dai na da nasaba da yadda ake samun tarin dalibai da basu da cikakkiyar gogewa a fannin na ilimin fasahar na'urar Computer, lamarin da ke zama tarnaki ga tsarin koyo da koyarwar zamani da komi ke shirin komawa tsarin amfani da na'urar ta computer.

    Ku latsa alamar sauti don saurarin cikakken shirin...................

    11 min

About Ilimi Hasken Rayuwa

From the publisher's feed

Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken…

More shows like Ilimi Hasken Rayuwa

Labarai by RFI Hausa

Labarai

0 Listeners

Kasuwanci by RFI Hausa

Kasuwanci

0 Listeners

Muhallinka Rayuwarka by RFI Hausa

Muhallinka Rayuwarka

0 Listeners

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare by RFI Hausa

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

0 Listeners

Lafiya Jari ce by RFI Hausa

Lafiya Jari ce

0 Listeners

Wasanni by RFI Hausa

Wasanni

0 Listeners

Dandalin Fasahar Fina-finai by RFI Hausa

Dandalin Fasahar Fina-finai

0 Listeners

Tarihin Afrika by RFI Hausa

Tarihin Afrika

0 Listeners

Al'adun Gargajiya by RFI Hausa

Al'adun Gargajiya

0 Listeners

Tambaya da Amsa by RFI Hausa

Tambaya da Amsa

0 Listeners